Header Ads

Bidiyon cin zarafi: Kwamishinan 'yan sanda a jihar Ribas ya bayar da umarnin kamo jami'an 'yan sanda

Dan sandan a yayin da ya ke cin zarafin mutumin mara laifi

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Ribas, CP Okon O Effiong, ya bayar da umarnin a kamo jami'an 'yan sandan da aka gani a cikin wani bidiyo suna cin zarafin wani mutum.

Wannan ya biyo bayan gane 'yan sandan da ke cikin wani bidiyo ne wadanda ke cin zarafin wani mutum da ba a iya gane ko waye ba a Elibrade junction, Emohua da ke Fatakwal.

Kwamishinan 'yan sandan a cikin wani jawabi ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan, SP Grace Iringe-Koko, ya bayyana cewa a matsayinsa na mai kare hakkin bil-adama, yana tabbatarwa mutanen kasa cewa jami'an 'yan sandan za a bincike su kamar yadda dokar aikin jami'an 'yan sanda ta tanadar, tare da samar da hukuncin da ya dace.

Ya ma kara da tabbatarwa mutanen jihar Ribas cewa za su tabbatar da ana bin doka.

"Ana bukatar mutane su kawo rahoton cin zarafin bil-adama da keta hakkoki ta wadannan nambobi: 08039213071 da kuma 08098880134." Kamar yadda ya bayyana.

A dai ranar Litinin ne a wani bidiyo aka ga wani dan sanda yana marin wani mutum akai-akai a Fatakwal ya kuma tursasa masa shiga cikin wata mota.

No comments

Powered by Blogger.