Header Ads

Bayan karbar kudin fansa, an sako daliban makarantar Yauri da 'ya'ya biyu

Daliban da aka fanso gun 'yan bindigan

Bayan karbar kudade masu yawa a matsayin kudin fansa, sanannen shugaban masu garkuwa da mutane, Dogo Daji, ya sako hudu daga cikin dalubai 11 da suka rage na Kwalejin gwamnatin tarayya ta 'yan mata da ke Yauri a jihar Kebbi.

Kamar yadda PRNigeria ta ruwaito, biyu daga cikin 'yan matan sun dawo da 'ya 'ya biyu wadanda suka haifa a yayin da ake tsare da su a can.

Dogo Daji ya dage a kan cewa sai gwamnatin jihar Kebbi ta cika wasu sharudda kafin a sako sauran 'yan matan.

Majiyoyinmu sun shaida mana cewa dole ne ya zamanto iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su hada kudaden fansar in har gwamnatin jihar Kebbi ba ta yi abinda masu garkuwa da mutanen ke so ba.

Iyayen dole su roki 'yan Nijeriya da su kawo masu taimako na kudi domin su ceto 'ya 'yansu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

A cikin wata wasika da suka rubuta zuwa ga 'yan Nijeriya a cikin watan Janairun shekarar 2023, kuma wadda PRNigeria ta samu, wata kungiya ta iyayen daluban 11 da aka yi garkuwa da su mai suna "Committee of Parents of 11 Abducted Students of F.G.C Birnin Yauri, Kebbi State, Nigeria" sun yi roko da a hada kudi har naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa domin 'ya 'yan su su dawo.

A cikin wasikar, shugaba da kuma sakataren kungiyar iyayen yaran, Salim Ka'oje da Mista Daniel Alkali, sun bayyana cewa 'ya 'yansu (wadanda shekarunsu suka kama tsakanin 12 - 16) suna tsare a hannun wadanda suka yi garkuwa da su a tsawon watanni 20 kenan.

"... Kuma wadanda suka yi garkuwa da su din suna neman naira miliyan 100 ne kafin su saki 'yan matan." Kamar yadda suka bayyana.

In dai za a iya tunawa, an sace 'yan matan 11 ne bayan 'yan bindigan sun afka makarantarsu a ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2021.

A cikin watan Nuwambar da ta gabata, PRNigeria ta ruwaito cewa wasu daga cikin 'yan matan sun zama iyaye masu kananan shekaru a yayin da hudu daga cikinsu suna da ciki.

Sai dai PRNigeria ba iya tabbatar da ko kudin da iyayen 'yan matan suka biya sun kai har miliyan 100 kamar yadda masu garkuwar ke bukata ba.

No comments

Powered by Blogger.