Header Ads

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya cika shekaru 84 masu albarka

Ayatullah Ali Khamene'i 

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya cika shekaru 84 masu albarka a duniya a ranar 19/4/2023.

An dai haifi Sayyid Khamenei ne a ranar 19 ga watan Afirilun shekarar 1939 a garin Mashad da ke kasar Iran, kuma sunan mahaifinsa Javad Khamenei, mahaifiyarsa kuwa sunan ta Khadijeh Mirdamadi. 

Allah Ya albarkace babban jagoran na kasar Iran da 'ya'ya shida da mata daya. 'Ya'yan nasa sune Mostafa, Mojtaba, Masoud (Mohsen), Meysam, Hoda da kuma Boshra, wadanda kuma dukkansu malamai ne.

A matsayinsa na wanda ya fi kowanne shugaba iko a kasar Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ne babban kwamandan sojojin kasar Iran, zai iya yanke hukunci kai tsaye ya kuma fadi matsaya ta karshe a fannin tattalin arzuki, muhalli, harkokin kasashen waje da tsarin kasar Iran. A matsayinsa na babban shugaba, yana da iko kai tsaye ko ba kai tsaye ba a sashen zartarwa, majalisar dokoki, sashen shari'a, soja da sashen jarida kamar yadda Karim Sadjadpour, wani mai nazari a kan siyasa a kasar Iran, ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.