An samu ɗan takarar gwamnan Enugu karkashin APGA da ya bace kwanaki kwance a kasa ba rai
An gano dan takarar kujerar gwamna a zaben gwamna da aka kammala a kwanakin baya a jihar Enugu wanda aka bayyana cewa ya bace, Dons Udeh, a kwance ba rai.
Udeh, wanda aka bayyana cewa ya bace tun ranar Asabar, an gan shi ne kwance ba rai a yankin 9th mile da ke Enugu.
Kafin rasuwarsa, marigayin ya yi fatar zama gwamnan jihar ta Enugu a karkashin jam'iyyar APGA.
Kamar yadda wata majiya daga iyalinsa ta bayyana, an gano mota da wayar marigayin tun tuni, 'yan sanda ba su fitar da wani jawabi a hukumance ba kan al'amarin tukunna.
Post a Comment