Header Ads

An kashe daya daga cikin mambobin Majalisar Kwararru ta Iran a arewacin kasar

Shahid Ayatollah Abbasali Soleimani

An kashe wani mamba a majalisar malamai mai matukar muhimmanci ta Iran a yayin wani harin makami da aka kai a yankin arewacin kasar Iran na Mazandaran.

Ayatollah Abbasali Soleimani, wanda mamba ne a Majalisar Kwararru ta Iran kuma tsohon wakilin shugaban juyin-juya hali na kasar Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei a kudancin kasar Iran a Sistan da Baluchistan, ya yi shahada ne a asibiti a ranar Laraba bayan an harbe shi a banki a birnin Babolsar, kamar yadda kafar watsa labaru ta Mehr ta ruwaito.

Babban gwamnan yankin Mazandaran, Seyyed Mahmoud Hosseinipour, ya shaidawa kafar watsa labaru ta gidan talabijin mallakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRINN) cewa ana kan bincike domin gano ko me kenan dangane da mummunan al'amarin da kuma dalilin aiwatar da kisan.

Majalisar Kwararrun dai suna zaba ne tare da kula da al'amurran shugaban Juyin-juya Hali na Musulunci, kuma suna da matsayi da za su nada ko kuma su cire shugaban.

Mambobin dai mutane ke zabar su domin su shiga ofishi kai tsaye har na tsawon shekaru takwas. Majalisar na yin zama domin tattaunawa kan al'amurran kasa sau biyu a shekara sannan kuma sukan nada sabon shugabansu a duk shekara.

No comments

Powered by Blogger.