Header Ads

An harba makaman roka da dama cikin Isra'ila daga Lebanon a matsayin gargadin Hezbollah ga Isra'ila


Akalla makaman roka 30 aka harba daga kudancin kasar Lebanon zuwa yankunan da Isra'ila ta mamaye a matsayin mayar da martani kan harin da Isra'ila ta kai harabar masallacin al-Aqsa a tsawon dare da kuma harin ta kan Falasdinawa masu gabatar da ibada a cikin watan Ramadan.

Kamar yadda kafar watsa labarun Isra'ila, KAN, ta bayyana, makaman rokan sun fada yankunan Western and Upper Galilee ne inda aka samu raunuka da lalacewar abubuwa.

Kafar watsa labarun ta bayyana cewa sauran makaman rokan na'urar Iron Dome Missile ta kabo su kasa. 

Bangaren sojojin Isra'ila ba su bayyana makaman rokan ko guda nawa ba ne.

Wannan harin shine wanda ya fi kowanne girma da aka harbo makaman roka daga Lebanon tun bayan yakin kwanaki 33 da aka yi a cikin shekarar 2006 a tsakanin kungiyar fafutika ta Hezbollah da ke Lebanon da kuma Isra'ila, inda aka harbo dubunnan rokoki zuwa kasar mamayar.

A cikin watan Agustan shekarar 2022, kungiyar ta Hezbollah ma ta harba makaman roka 19 arewacin Isra'ila.

No comments

Powered by Blogger.