Allah ya ji kan Matar Aminu Dantata, Hajiya Rabi, da ta rasu a Saudi Arabiya
Hajiya Rabi, wadda mata ce ga Alhaji Aminu Dantata, wani sanannen dan kasuwa a Nijeriya, ta rasu bayan doguwar jinya.
Da safiyar ranar Lahadi, jikan marigayiyar, Sanusi Dantata, ya tabbatar da hakan a shafin sa na Twitter, inda ya bayyana cewa, "Don Allah ku yi addu'a ga mahaifiyarmu, kakarmu, kakar-kakarmu, Haj. Rabi, matar Alh. Aminu Dantata, wadda ta rasu jiya bayan doguwar jinya!
"Muna fata Allah Ya yi mata rahama, Ya karbi kyawawan ayyukanta, ya kuma ba ta matsayi mai girma a gidan Aljannah, Ameen!
"Innalillahi Wa Inna Ilaihirraji'un!"
Marigayiyar, wadda aka fi sani da Mama Rabi, itace mahaifiyar Tajuddeen Dantata, daya daga cikin sanannun 'ya'yan Dantata.
An dai bayyana cewa ta rasu ne a wani asibiti da ke Jiddah, masarautar Saudi Arabiya, bayan doguwar jinya.
Ta rasu tana da shekaru 70 da wani abu, ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya shida, a cikinsu akwai Tajuddeen Dantata, Batulu Dantata, Hafsa Dantata, Jamila Dantata da Aliya Dantata.
Marigayiyar na da jikoki da dama.
Post a Comment