Alkalin wata babbar kotun Abuja ya kori ƙarar neman a bai wa Sheikh Zakzaky fasfonsa
Alkalin babbar kotu da ke Abuja (Federal High Court), Alkali Obiora Atuegwu Egwuta, a ranar Alhamis, 30 ga watan Macin shekarar 2023, a yayin da yake yanke hukunci a kan shari'ar fasfo din shehin malami, Sheikh Ibraheem Zakzaky da na mai dakinsa, malama Zeenat, ya bayyana cewa wadanda suka kawo kara, wato bangaren Sheikh Zakzaky kenan da na mai dakinsa, ba su kawo hujjoji wadanda ya dace su kawo a shari'a domin ya bada odar a yi sabon fasfo ba, kamar yadda daya daga cikin lauyoyin malamin, Haruna Magashi, ya bayyana a cikin wata tattaunawa da kafar ABS ta yi da shi a cikin wani bidiyo wanda ta sa a kafar sada zumunta ta Facebook.
Shehin malamin ya shigar da karar hukumomin DSS, NIA, NIS da Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami, ne kan hana masa fasfo dinsa na yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, wannan fasfo kuwa samun sa shi zai bayar da dama ga shehin malamin da mai dakinsa su fita zuwa kasar waje domin samun cikakkiya kulawar likitoci ga lafiyarsu sakamakon harbin su da harsasai da aka yi tun cikin shekarar 2015 lokacin da rundunar jami'an tsaron Nijeriya suka afkawa almajiransa maza, mata, yara da tsofaffi a Husainiyya Baqiyyatullah, gidan shehin malamin da ke gyallesu, Islamic Center da makabartar Darur Rahama duka da ke Zariya a jihar Kaduna da kisa.
Kamar yadda ya ke a cikin tattaunawar, daya daga cikin lauyan malamin, Haruna Magashi, ya bayyana cewa, "Da ma kamar yadda aka sani an sa yau ne domin yanke hukunci bayan sauraron dukkan bangarorin shari'a, bayan sauraron duka kesa-kesan guda biyu, daya na Malam daya na Malama, bayan alkalin ya zauna ya yi hukuncin nasa, to abinda masana kuma suke kallo a matsayin wani abu daban kuma sai ya zamana ya juya hukuncin ya ce wadanda suka kawo kara, bangaren malam kenan da malama, wai basu kawo hujjoji wadanda ya dace su kawo a shari'a domin ya ba da odar a yi sabon fasfo ba.
"Ya kawo cewa akwai maganganu guda biyu, da muka yi, na farko mun ce an je Indiya, sannan muka dawo mu ka ce fasfo ya kone a lokacin waki'a, to sai ya yi amfani da wannan ya ce maganganunmu sun yi karo, saboda haka hujjojin ba su tsaya ba bayan kuma a zahirin gaskiya babu wani karo a maganar tunda al'amarin ne da ya faru duk muka kawo shi a rubuce, cewa da farko mun nemi a ba da fasfo saboda fasfo yana hannun jami'an gwamnati kuma sun ce ya bata, daga baya kuma muka sake yin affidavit cewa tun farko ma me ya kai fasfo wajen su, shine lokacin waki'a din an kone fasfo din su malam dan haka lokacin da za a tafi Indiya a shekarar 2018 sai aka sake yin wani fasfo na biyu wanda reissuance ne, aka yi amfani da shi aka je Indiya aka dawo, to kuma duk tafiya Indiya, tun daga tafiya har dawowa fasfo yana hannun jami'an tsaro kuma ba su ba su malam ba.
"Yanzu da aka bukata suka ce babu fasfo a hannun su, to abinda muka nusar da shi alkalin kenan, amma sai ya rufe idon sa daga cewa mun yi magana an ba da fasfo a 2018, kawai sai ya tsaya cewa shi ya ga karo a maganganunmu bayan kuma duk wanda ya duba zai ga babu wani karo, to shi ne dai abinda ya faru ya yi hukunci cewa ba zai ba da oda a sake yiwa su Malam fasfo ba."
Da aka tambayi lauyan shin za a sake shigar da wata karar ne ko wane mataki za a dauka? Sai ya bayyana cewa, "Idan aka samu haka a shari'a abu na farko da lauyoyi ke yi shi ne za su karbi kwafi na hukuncin da kuma shari'ar ma baki daya a sake bibiyarsu sannan su fitar da shawarar da suke ga ya dace na matakin da za a sake dauka, daga nan sai a gabatar da su Malam, sannan su malam su ne suke da cewa ga abinda za a yi a nan gaba, amma dai a maganar appeal mun karfafa cewa lallai za a daukaka kara za a yi appeal to abinda mu ka shirya kenan muka gabatar da su malam, to muna saurare me su malam za su ce a yi, duk abinda suka dora kuma shi kenan shi za a yi."
Da ya ke amsa tambayar ko akwai wani abu na gaggawa da za a iya yi ko haka za a jira har sai lokacin da ta sake wani zaman, ganin cewa su malam na fama da jiki kuma akwai bukatar shi wannan fasfo wajen fita waje, sai lauyan nasa ya amsa da cewa, "To tunda shi alkali ya yi hukunci, to sai idan wata kotun ta sama kenan ta juya hukuncin, shine za a iya, amma yanzu ba za a dauki wani matakin shari'a ba sai dai a yi appeal a kan abinda ya faru, sai dai kuma ta yiwu akwai wasu hanyoyin da za a iya dauka domin samun natijar abinda ake nema."
Post a Comment