Ɗaliban jami'ar Ahmadu Bello sun shiga wani hali sakamakon rashin wutar lantarki
Daluban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna sun shiga wani hali sakamakon rashin wutar lantarki a jami'ar.
Wannan rashin wutar lantarki wanda ya jefa daluban cikin wani hali ya samo asali ne bayan matakin da hukumar kula da wutar lantarki ta jihar Kaduna ta dauka na yanke wutar lantarkin jami'ar kai tsaye saboda laifin rashin biyan bashi wanda ya kai har naira miliyan dari tara da talatin da daya da dubu dari biyar da saba'in da tara da dari uku da sha bakwai (931,579,317).
To sai dai wannan mataki duk da cewa ya shafi dalubai a jami'ar ba kan su kadai ya tsaya ba, domin kuwa ya shafi sauran al'ummar da ke zaune a jami'ar ma baki daya.
Rashin wutar lantarkin ya haddasa rashin ruwa da abubuwa da dama wadanda bil-adama ke bukata musamman ma dalubi.
Wata dalubar jami'ar wadda ta nemi a sakaya sunan ta ta bayyana cewa ya kamata hukumomi da kungiyoyin tsoffin daluban jami'ar su shigo cikin al'amarin rashin wuta a jami'ar domin gudun samun tsaiko ga karatun daluban.
Wannan al'amari dai ya faru ne a karkashin mulkin mukaddashin shugaban jami'ar, Farfesa Kabiru Bala.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, bincike ya nuna cewa an ga shugabannin kungiyoyin dalubai na tattaunawa a kan al'amarin.
Post a Comment