Header Ads

Zulum ya samu nasarar tazarce a jihar Borno

Gwamna Zulum ya lashe zaben gwamnan Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya sake samun nasarar komawa wa'adi na biyu na mulkin jihar, bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamna da aka gudanar a ransar Asabar ɗin da ta gabata.

INEC ce ta bayyana ɗan takara a matsayin wanda ya lashe zaɓen a Maiduguri babban birnin jihar a ranar Litinin.

Zulum ya lashe zaɓen ne da ƙuri'a 545,542 sai kuma jam'iyyar PDP ta ke da ƙuri'u 82,147.

Jam'iyyar LP wadda ta taka rawar gani a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabirairu ta zo ta uku da kuri'a 1,517.

No comments

Powered by Blogger.