Header Ads

Zazzaɓin Lassa: Mutanen da suka rasa rayukansu a Nijeriya sun kai 104 a 2023

Wasu beraye da kawo cutar Lassa

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Nijeriya (NCDC) ta bayyana cewa mutane 104 ne suka rasu sanadiyyar zazzabin Lassa yayin da wasu 636 kuma suka kamu da cutar daga watan Janairu zuwa 26 ga watan Fabrairun shekarar 2023 a fadin Nijeriya.

Hukumar ta bayyana cewa an auna yanayin rasuwar da mutane ke yi da abinda ake kira case fatality rate (CFR) inda ya kasance kashi 16.8 cikin 100 na masu cutar ke mutuwa sakamakon cutar, wanda hakan bai kai kashi 18.1 cikin 100 na masu mutuwa sakamakon cutar ba a kamar daidai wannan lokacin a shekarar 2022.

Wadannan bayanan na kunshe ne a cikin rahoton yaduwar cuta na hukumar wanda suka sa a shafin su na yanar gizo, wanda bayanin na sati na 8 ne a cikin shekarar 2023, daga 20 zuwa 26 ga watan Fabrairu.

Rahoton ya nuna cewa mutane 351 ake zargin sun kamu da cutar a cikin satin da ake yin bincike a kai, mutane 59 sun kamu kuma wasu 10 sun rasa rayukansu sakamakon zazzabin. 

A dai cikin shekarar ta 2023, kamar yadda rahoton ya bayyana, akalla mutum daya an tabbatar da cewa ya kamu a cikin kananan hukumomi 88 da ke cikin jihohi 22, bayan haka a cikin duk wadanda aka tabbatar suna da cutar, kashi 70 cikin 100 daga jihohin Ondo, Edo da Bauchi suke. 

Jihar Ondo, wadda ta ke a kudu maso yammacin kasar Nijeriya, itace a saman jerin da aka yi, inda ta ke da kashi 33 cikin 100, a yayin da jihohin Edo da Bauchi ke da kashi 28 da kashi 9 a cikin 100 na wadanda suka kamu.

Zazzabin Lassa cuta ce mai haifar da zubar jini da yawa wadda ke samun mutane ta hanyar yin tu'ammali da abinci ko sauran kayayyakin gida wadanda beraye suka bata ko kuma mutanen da suka kamu.

Alamomin zazzabin sun hada da zazzabi, ciwon kai, jin daci a harshe, kasalar jiki, tari, jiri, amai, gudawa, rashin jin karfin gabobi da cwon kirji, yayin da zazzabin na Lassa ya ta'azzara sai jini ya fara fitowa ta idanu, kunnuwa, hanci, baki da sauran kofofin jiki.

No comments

Powered by Blogger.