Header Ads

Zazzabin Lassa: Mutane 142 sun rasa rayukansu a cikin jihohi 23

Wasu beraye

Hukumar hana yaduwar cututtuka, maganinsu da rigakafinsu ta Nijeriya (NCDC) ta bayyana cewa mutane 142 suka rasa rayukansu a cikin jihohi 23 a Nijeriya tun bayan shigowar wannan shekarar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta a ranar Talata, inda ta bayyana cewa wadannan jihohi 23 suna da akalla mutum daya da ya kamu da zazzabin a cikin kananan hukumomi 97.

Kamar yadda rahoton ya nuna, "Kashi 71 cikin 100 na wadanda aka tabbatar suna da zazzabin lassa din sun fito ne daga jihohin Ondo, Edo da Bauchi."

Kashi 29 cikin 100 su kuma daga jihohin da aka tabbatar da cewa cutar ta bulla. A cikin kashi 71 cikin 100 da aka tabbatar, jihar Ondo na da kashi 32 cikin 100, Edo na da kashi 29 cikin 100 sai kuma Bauchi da ke da kashi 10 cikin 100.

Da aka kwatanta rahoton wannan shekarar da na shekarar da ta gabata, wadanda ake zargin suna da zazzabin ya karu a wannan shekarar.

"Wadanda ake zargin suna da zazzabin sun karu in an kwatanta da shekarar da ta gabata ta 2022 a daidai wannan lokacin."

Rahoton ya ma nuna cewa matasa sun fi hatsarin kamuwa da cutar, inda rahoton ya nuna cewa wadanda suka fi kamuwa da cutar sune mutanen da suke a tsakanin shekarun 21 zuwa 30.

Zazzabin lassa dai zazzabi ne mai haifar da zubar jini da yawa wanda ke samun mutane ta hanyar yin tu'ammali da abinci ko sauran kayayyakin gida wadanda beraye suka bata ko kuma mutanen da suka kamu.

Alamomin zazzabin sun hada da ciwon kai, jin daci a harshe, kasalar jiki, tari, jiri, amai, gudana, rashin jin karfin gabobi da ciwon kirji, yayin da zazzabin na lassa ya ta'azzara kuma sai jini ya fara fitowa ta idanu, kunnuwa, hanci, baki da sauran kofofin jiki.

No comments

Powered by Blogger.