Zan tabbatarwa kotu cewa an murde zaben shugaban kasa ne domin Tinubu ya yi nasara - Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP (Labour Party) a zaben da aka kammala ranar Asabar da ta gabata a Nijeriya, Peter Obi, ya bayyana cewa zai tabbatarwa 'yan Nijeriya a kotu cewa shi ya ci zabe.
Ahmed Bola Tinubu ne dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana ranar Laraba a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar wanda aka gudanar ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.
A yayin da ya ke magana a wurin wani taron 'yan jaridu a ranar Alhamis, Peter Obi ya bayyana cewa an bukace shi da ya je kotu in har yana da koke, kuma abinda zai yi kenan.
"Kun san cewa ni ina da biyayya, sun bukaci in je kotu kuma abinda zan yi kenan." Obi ya bayyana.
A yayin da aka tambaye shi ya samar da hujjarsa ta cewa zaben ba sahihi bane, sai ya ce zai tabbatarwa 'yan Nijeriya a kotu cewa an yi magudi a cikin zaben.
"Sai na kalubalanci tsarin." Ya tabbatar.
"Wannan ba domin ni ba kawai, sai domin nan gaba."
Post a Comment