Header Ads

Zan kasance bawa ba shugaba ba ga 'yan Nijeriya - Tinubu


BAT ke nan, wato Bola Ahmad Tinubu

Zababben shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa zai kasance bawa ga 'yan Nijeriya ba shugaba ba, kuma Nijeriya na da sabuwar fata a yanzu.

Tinubu, wanda ya bayyana haka a ranar Laraba yayin da ya ke jawabin nuna amincewa da zabensa, ya bayyana cewa wannan wani nauyi ne aka dora masa kuma ya dauka domin ya yi aiki ga 'yan Nijeriya.

"Wannan wani nauyi ne kuma na dauka domin in yi maku aiki, in zama bawa a gareku ba shugaba a gareku ba, in yi aiki tare da ku domin mayar da Nijeriya kasaitacciya.

"Ina kira ga wadanda muka yi takara tare, mu hadu mu yi aiki tare, wannan kasar ce kawai muke da ita, mu hadu mu gina ta a tare, mu dinke barakar da ta ke a tsakaninmu, mu yi aiki domin samar da farin ciki, hadin kai da zaman lafiya."

Tinubu, wanda ya bayyana cewa zai yi aiki da wadanda ya yi takarar da su, ya ce Nijeriya ta na da abinda ake bukata domin samar da cigaba da mayar da ita wani wuri wanda kowa ke son zuwa.

Da ya ke magana dangane da bangaren matasa kuwa, ya bayyana abubuwan da zai yi ga bangaren ilimi, inda ya ce, "Zan mayar da hankali sosai a bangaren ilimin ku, karatun da ya kamata a yi a cikin shekara hudu za a yi shi a cikin shekara hudu, ba sauran yajin aiki kuma, jami'o'i za su samu 'yancin kansu, ba sauran sayar da jadawalin karatu ga dalubai (handouts), malamai dole su zama marubuta. Na san me ke yi maku ciwo, kuma na yi imani za ku ga amfanin zaben da kuka yi." Zababben shugaban kasar ya yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a cikin jawabin nasa, inda ya bayyana shi da mai kishin kasa.

No comments

Powered by Blogger.