Header Ads

ZAƁEN SANATAN YOBE TA KUDU BAI KAMMALA BA


Wasu masu neman a bayyana sakamakon zaɓen a Potiskum

Daga Yusuf Waliy, Yobe
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta bayyana zaɓen ‘yan majalisar dattawa Wakilai daya gudanar a yankin Yobe ta kudu a matsayin wanda bai kammala ba.

Jami’in Hukumar Farfesa Shettima Abdulkadir Saidu ne ya sanar da haka a garin Potiskum a yau Litinin.

A cewarsa sun soke sakamakon zaɓen a mazabar 003 Manawaci da ke karamar hukumar Fika inda jimillar kuri’un da aka kada ya zarce a dadin wadanda aka tantance.

Al'umma sun wuni a gaban Ofishin Hukumar Zaben a garin Potiskum don nuna damuwarsu da rashin bayya sakamon zaɓen

No comments

Powered by Blogger.