Header Ads

Zaben gwamna a jihar Kaduna: Sakamakon zabe bai yi nuni da abin da mutane ke so ba - Dan takarar jam'iyyar PDP

Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, Isah Ashiru

Kusan kwana daya bayan bayyana sakamakon zaben jihar Kaduna, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP, Isah Ashiru, ya bayyana cewa sakamakon zaben bai yi nuni da abinda mutane ke so ba.

A dai ranar Litinin ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta ta bayyana dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Uba Sani, a matsayin wanda ya lashe zaben jihar da kuri'u 730,002, a yayin da babban abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Isah Ashiru, ya samu kuri'u 719,196, mai takarar gwamnan a karkashin jam'iyyar LP, Jonathan Asake, ya zo na uku da kuri'u 58,283 a yayin da dan takarar jam'iyyar NNPP, Suleiman Hunkuyi, ya samu kuri'u 21,405.

Sai dai a cikin wata sanarwa wadda mataimakin daraktan watsa labarai da hulda da jama'a na kamfe din dan takarar jam'iyyar ta PDP, Rueben Buhari, ya sawa hannu, dan takarar jam'iyyar ta PDP ya bayyana cewa duka magoya bayansa da mambobin jam'iyyar sa da suke bukatar kyakkyawan shugabanci a jihar su kwantar da hankalinsu su kuma zauna lafiya duk da yadda sakamakon zaben ya kasance.

"Mutanen da suka yarda da irin kudurin jam'iyya ta da kuma abinda na tsaya ma wa sun bayar da lokacin su, sun nuna sadaukarwa kuma sun yi aiki tukuru a kan tafiyarmu." Ashiru ya bayyana.

"Duk da matsalolin da aka samu na karancin mai, karancin kudi, rashin tsaro da barazana duk da haka mutane sun fita sun yi zabe. Kuma duk da cewa an yi ta daga lokaci kafin a fadi sakamakon zaben, sun yi hakuri sun jira a hankali kwance.

"Ina godiya ga irin wadannan abubuwa da suka yi da kuma goyon bayansu, musamman shawarwarinsu a gare ni." 

Dan takarar ta jam'iyyar PDP ya bayyana cewa shi da mambobin jam'iyyarsa suna duba duk yadda al'amarin zaben ya gudana, ciki harda sakamakon zaben wanda gabadaya bai yi daidai da abinda mafi yawan jama'ar jihar Kaduna da suka yi zabe suke so ba, wanda ya ce wannan shine zai samar da tushen matakin da shi da kuma jam'iyyar sa za su dauka na gaba.

Dan takarar ya kara da yin godiya ga mambobin jam'iyyarsa da magoya bayansa kan lokacin da suka bayar da abubuwan da suka mallaka a yayin gudanar da zabe a jihar, inda ya bayyana cewa irin sadaukarwa, yin aiki tukuru da kwarin gwiwa da mutane suka nuna ciki harda 'yan siyasa, ya sa shi murna matuka.

No comments

Powered by Blogger.