Yawan wadanda jami'an tsaro suka kashe a Kaduna yayin muzahara ya karu
Da yammacin jiya Alhamis ne 'yan'uwa musulmi, mabiya Shaikh Zakzaky suka fito kan titi domin kira ga gwamnati a kan ta sakar wa malaminsu fasfo ɗinsa na fita kasar waje domin neman magani.
'Yan'uwa musulmi dai sun fito suna faɗin "Free Zakzaky fasfo" daga Gwamna road a kan titin Western bypass da me Kaduna, suna cikin tafiya a daidai Bakin Ruwa, sai jami'an tsaro suka iso wajen su suna harba musu tiyagas da bindiga mai harsashi mai rai. Haka ya yi sanadiyyar shahadar mutane shida a cikin 'yan'uwa tare da wasu jama'an gari akalla mutum uku, baya a raunata da dama..
HOTUNA TARE DA SUNAYEN SHAHIDAN MU..
'Yan'uwa musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky da jami'an tsaro bisa umarnin gwamna Nasuru Elrufa'i suka kashe a Kaduna a yammacin Alhamis 16 ga watan Maris, 2023.
1. Shaheed Ali Sulaiman
2. Shaheed Yaseer Isma'il Abdul'aziz
3. Shaheed Abdulmalik Ibrahim Yawale
4. Shaheed Abubakar (Abba) Nura
5. Shaheed Ibraheem Abdul'aziz
Post a Comment