Header Ads

YANZU-YANZU: An yi Jana'izar Shattiman Potiskum

Dandazon jama'ar da ta halarci janazar Shattiman Potiskum

       -Daga Yusuf Waliy

Da misalin karfe 2:00 na ranar yau Litinin aka yi Jana'izar Marigayi Alhaji Mamman Tela. Alhaji Tela, Dattijo ne mai shekaru kuma kafin rasuwarsa shi ne Shattiman Pataskum.

Ya rasu ne sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita. Taron Jana'izar ya gudana ne a kofar fadar Sarkin Pataskum Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, da ke Yarimaram a cikin garin Potiskum ta Jihar Yobe.

Daruruwan al'umma ne suka taro ya yin Jana'izar da suka hada da Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Idi Barde, wanda ya Wakilci Gwamnan da kuma Sarakuna da dama na Jihar Yoben.

No comments

Powered by Blogger.