Header Ads

'Yan sanda sun yi magana kan cin zarafin da sojojin ruwan Nijeriya su 15 suka yi wa wani saje dan sanda


Kwamishinan 'yan sanda a jihar Delta, Muhammed Ali

'Yan sanda a jihar Delta, wadda jiha ce da ke kudu-maso-kudu a Nijeriya, sun yi magana a kan cin zarafin da aka yiwa wani dan sanda a ranar 9 ga watan Maci, inda wasu sojojin ruwa na Nijeriya suka afka ofishin 'yan sandan.

Kamar yadda PREMIUM TIMES ta bayyana wadda ta dogara da wani bidiyo wanda aka sa a kafar Twitter, sun yi rahoto a kan al'amarin wanda ya faru a Enerhen, kusa da Warri.

Bidiyon, wanda ke da tsawon minti 1 da sakonni 30, ya nuna jami'in dan sanda wanda aka ciwa zarafi yana kai da koma a cikin ofishin 'yan sandan tare da 'yan uwansa fusatattu wadanda ke rokonsa ya kwantar da hankalinsa.

A cikin bidiyon, jini ya rufe fuskar dan sandan kuma kakinsa na 'yan sanda a yage ya ke.

Mai magana da yawun 'yan sanda a jihar, Bright Edafe, a cikin wani jawabi, ya bayyana cewa jami'an sojojin ruwa 15 ne suke da alhakin cin zarafin dan sandan.

Ya bayyana cewa harin wani soja ne mai suna Kevwe Ejaita ya jagorance shi, wanda suka yi hatsaniya da jami'in dan sandan, kwana daya bayan hakan shi ne suka zo su duke shi har cikin ofishin 'yan sanda.

"DPO din ofishin na 'yan sanda a nasa bangaren sai ya yunkura shima da mutanensa kuma suka hana kaddamar da harin, shi kuwa wanda ya jagoranci harin, Kevwe Ejaita, an kama shi.

"Bayan an sanar da sashen sojojin ruwa da ke Warri al'amarin, sai suka tada tawagar 'yan sanda na cikin sojoji domin zuwa ofishin 'yan sandan. Sun karbi sojan tare da tabbatar da cewa za su ladaftar da shi. Shi kuma dan sandan wanda aka raunata sai aka tafi da shi asibiti domin duba lafiyarsa, daga baya kuma aka sallamesa." Kamar yadda Mista Edafe, wanda ya ke mataimakin sufiritandan 'yan sanda ya bayyana. 

A cikin bayanin, ya bayyana cewa sojojin na ruwa da 'yan sandan na aiki tare domin hana afkuwar hakan a nan gaba.

A cikin jawabin ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Delta, Muhammed Ali, ya yi Allah wadai da abinda sojojin ruwan suka yi, inda ya bayyana cewa "cin zarafin dan sanda a yayin da yake a bakin aikinsa ba za a amince da shi ba."

No comments

Powered by Blogger.