Header Ads

'Yan sanda sun ƙaryata labarin kai wa gidan Shugaban INEC hari


Gidan da mafusata suka aukawa a Bauchi

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa hasalallun matasa sun kai wa gidan Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu hari a Bauchi.

Tun daga ranar Juma'a ce aka riƙa yaɗa wani faifan bidiyo a soshiyal midiya, inda aka nuno cincirindon matasa a ƙofar wani gida su na jifa.

Gidan an riƙa danganta shi da cewa gidan Yakubu ne, Shugaban INEC da ke Bauchi.

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labaran 'Yan Sandan Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, ya shaida wa manema labarai cewa gidan ba na shugaban hukumar zaɓe ba ne.

Cikin sanarwar da Wakil ya raba wa manema labarai a ranar Asabar, ya bayyana cewa: "Mu na so mu fayyace wa jama'a wannan abu da ya faru ba ma a Jihar Bauchi ba ne kwata-kwata.

"Saboda haka danganta gidan da cewa na Shugaban INEC ko da ke Bauchi, ƙarya ce, jama'a su guje ta.

"Bisa la'akari da irin illar yaɗa irin waɗannan labarai na bogi, musamman a wannan lokaci na bayan kammala zaɓe, zai iya yin tasiri ko barazana ga zaman lafiya. 

"Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Bauchi ya bada umarnin a gaggauta binciken tushen bidiyon da aka riƙa yaɗawa har ana danganta ta shi da gidan Yakubu na Bauchi." 

Kwamishinan 'yan sandan Aminu Alhassan ya ce wanda duk aka kama da laifi zai fuskanci hukunci a kotu.

No comments

Powered by Blogger.