Header Ads

'Yan sanda a Indonesia sun kama 'yan Nijeriya uku, tare da gano hodar koken ta dalar Amurka miliyan 1.3

Jami'an Indonesia

'Yan sanda a kasar Indonesia a ranar Laraba 15 ga watan Maci, sun bayyana cewa sun kama 'yan kasashen waje mutum hudu, cikinsu kuma uku 'yan Nijeriya ne a yayin da suke kokarin shigar da kwayoyi cikin kasar. 

Kakakin 'yan sanda, Trunoyudo Wisnu Andika, ya bayyana cewa an kama 'yan Nijeriya a tsakanin watan Janairu da Maci a filin jiragen sama na kasa-da-kasa na Soekarno-Hatta a birnin Jakarta da kuma cikin wasu gidaje a bangarorin babban birnin kasar daban-daban.

Daya daga cikin 'yan Nijeriyan da aka kama an bayyana cewa ya hadiye kwayoyi masu yawa na Methamphetamine wanda nauyinsu ya kai kilogiram 2.2.

Gatot Sugeng Wibowo, shugaban hukumar kwastam da ke filin jirgin kasa-da-kasa na Soekarno-Hatta, ya bayyana cewa jami'ai sun kama Malachi Onyekachukwu Umanu, wani dan Nijeriya da ya zo filin jirgin kasan daga kasar Habasha a ranar 5 ga watan Maci ba tare da jaka babba ko karama ba.

Dabi'un da ya nuna suka sa aka fara zarginsa, jami'ai suka duba jikinsa, inda aka yi masa hoto wato X-ray, kuma aka samu kwayoyi 64 a cikin cikinsa. 

Hukumomi sun yi kokarin fito da kwayoyin daga cikinsa, wadanda ke dauke da kwayoyi masu karfi na Methamphetamine mai nauyin kilogiram 1.07 (pounds 2.3) a cikin kwana uku kamar yadda Wibowo ya bayyana. 

Jami'an na kwastam haka sun kama wani mutum dan kasar Brazil, Gustavo Pinto da Silveira, lokaci kadan bayan zuwansa daga Rio de Janeiro a farkon watan Janairu dauke da jakar hannu, jakar baya da kuma wani allo.

Daga farko ya ki yadda jami'ai su duba ko ruwan menene ya dakko a cikin kayansa.

Kin amincewar tasa ta sa jami'an suka duba ko menene wanda aka zuba a cikin kwalabe guda shida kuma mai matukar warin gaske. Binciken da aka gudanar a dakunan gwaje-gwaje ya nuna cewa ruwan lita biyu ne (67.7 ounces) na ruwan koken. 'Yan sanda sun ce kudinsu ya kai dalar Amurka miliyan 1.3.

Bayan haka 'yan sandar kasar ta Indonesia sun kama 'yan Nijeriya mutum biyu da kuma 'yan kasar ta Indonesia namiji da mace wadanda suke kokarin shigar da kwayoyin Meth daga kasar Indiya mai nauyin kilogiram 1.04 (2.2 pounds) wadanda aka nannade a cikin wani zani na leshi ta hanyar ofishin tura sakonni da ke birnin Jakarta.

No comments

Powered by Blogger.