Header Ads

'Yan Korea ta Arewa 800,000 sun sadaukar da kansu domin yaki da kasar Amurka - Rahoto

Gidan jarida mallakar kasar Koriya ta Arewa ya bayyana cewa dubunnan daruruwan mutanen kasar sun nuna yardarsu na shiga duk wani yaki wanda zai iya yiwuwa da kasar Amurka. 

A ranar Juma'a kawai, wasu 'yan kasar ma'aikata da dalubai da yawansu ya kai 800,000 sun nuna cewa sun sadaukar a dauke su ko kuma a sake daukarsu a cikin sojojin kasar domin yin wannan yaki, kamar yadda jaridar Rodong Sinmun ta ruwaito a ranar Asabar.

"Matasa sun yunkura domin yin kariya ga kasar mahaifansu, domin yakar abokan gaba da daidaita su." Kamar yadda rahoton ya nuna, ya kara da cewa, "'Yan mamayar Amurka da gwamnatoci 'yan amshin shatansu na so su wargaza 'yancinmu su kuma hana mana 'yancin mu rayu mu samu cigaba." 

"Tonon fada" daga Washington da Seoul "Sun wuce iyakar da za a iya yin hakuri da su" Koriya ta Arewa na so ta nuna cewa za ta iya "karya" duk wani karfi da sojojin makiya ke da shi, kamar yadda rahoton ya kara da cewa.

Kasar Amurka da Koriya ta Kudu sun yi atisayen sojoji daban-daban tun a farkon shekarar nan, duk kuwa da cewa kasar Koriya ta Arewa ta sha yin gargadi a garesu.

Kawayen junan sun kaddamar da atisaye na baya-bayan nan a ranar Litinin wanda suka yiwa lakabi da "Freedom Shield 23" kuma atisayen na kwana 11 ya kasance mai girman gaske fiye da na shekarar 2017, a wannan karon akwai atisayen kan kasa da kuma sauka a cikin ruwa.

Pyongyang na kallon wannan atisaye a matsayin gwaji na yadda za a afko cikin iyakokinta.

Domin mayar da martani, kasar Koriya ta Arewa ta kara kaimi wajen harba makamanta masu linzami a matsayin gargadi ga kawayen da su guji tonon fada a yankin na Koriya.

A cikin 'yan kwanakin baya, Pyongyang ta harba makaminta wanda zai iya kaiwa kowacce nahiya a duniya (ICBM) cikin tekun da ke tsakanin Koriya ta Arewa din da kasar Japan. 

A ranar Juma'a kuma kafofin watsa labarai na kasar suka saki bayanai da hotunan harbawar da aka yi wanda ya hada da makami mai linzami na kasar wanda zai iya kaiwa kowacce nahiya ta duniya mai suna Hwasong-17 ICBM wanda aka harba kwana daya kafin nan.

No comments

Powered by Blogger.