Header Ads

'Yan kasar Yemen sun kai karar kamfanonin makaman Amurka domin taimakon laifuffukan yaki


Mutanen kasar Yemen yayin da suke yin wata zana'ida ta wasu 'yan gida daya a ranar 8 ga watan Oktobar 2016, kwana daya bayan hare-haren jiragen sama da Saudiyya ke jagoranta ya samu gidan su da ke Bajil, yammacin yankin Houdeida.

'Yan kasar Yemen da ke zaune a Amurka sun shigar da karar manyan kamfanonin makamai na kasar Amurka wadanda suka hada da Raytheon, Lockheed Martin da General Dynamics, inda suka zarge su da "taikamakawa da tunzura aiwatar da laifuffukan yaki da kisa ba kan ka'ida ba" da kamfanonin ke yi ta hanyar samar da makamai ga hadakar kasashe da Saudiyya ke jagoranta wajen yin yaki a kasar Yemen.

Karar, wadda aka shigar a wata kotu da ke Washington DC, ta ma hada da sunayen shugabannin Saudi Arabiya da na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Mohammed bin Salman da Mohammed bin Zayed da kuma na Ministan Harkokin Kasashen Wajen Amurka, Antony Blinken da kuma sunan shugaban cibiyar Pentagon, Lloyd Austin.

"Shekara bayan shekara, ana jefa bama-bamai - a tarukan daurin aure, wurin zana'idar mutuwa, jiragen ruwan kamun kifi da motocin kwasar dalubai na makaranta - wannan ya yi sanadiyyar kashe dubunnan fararen hula hakan kuma ya taimaka wajen mayar da kasar Yemen wurin da ya fi muni wajen fuskantar bala'o'i da suka shafi bil-adama a duniya." Kamar yadda karar ta kunsa.

"Makamai wadanda kamfanonin Amurka ke sayarwa kuma wadanda manyan jami'an Amurka suka aminta da hakan, ya ba Saudi Arabiya da Hadaddiyar Daular Larabawa ta hanyar jami'an da aka ambata dama su jefa bama-bamai na rashin imani ba tare da lissafi ba." Kamar yadda ya ke a cikin karar

Wadanda suka shigar da karar 'yan kasar Yemen ne wadanda suka bayyana cewa suna wakiltar harin bama-bamai biyu ne wadanda hadakar kasashen da Saudiyya ke yiwa jagorancin suka kai a kasar - daya a shekarar 2015 yayin wani biki, dayan kuma a shekarar 2016 yayin da ake gudanar da wata zana'ida.

A cikin watan Oktobar 2015, iyalan al - Sanabani sun shirya tsaf domin gudanar da bikin taya wani daga cikin iyalan murnar aure da ya yi, kawai sai jirgin yaki ya sako bam wajen inda ya kashe mutane 43, wadanda suka hada da mata 13 da yara 16.

Shekara daya bayan wannan al'amari, a cikin watan Oktobar shekarar 2016, an jefa bam kan wata zana'ida wadda ta tara jama'a, a nan kuma mutane 100 suka rasa rayukansu. Kungiyoyin kare hakkin bil-adama na duniya a lokacin sun bayyana cewa bam din da aka yi amfani da shi mai suna GBU-12 Paveway II a Amurka aka kera shi.

Masarautar Saudi Arabiya da hadakar wasu kawayenta daga cikin kasashen larabawa tare da taimakon makamai da dabaru daga Amurka da wasu kasashen yammacin duniya, sun kaddamar da mummunan yakin ne a kasar Yemen cikin watan Macin shekarar 2015.

Manufar kuwa itace a kawar da kungiyar fafutika ta Ansarullah wadda ke kula da harkokin gwamnati bayan an rasa wata takamaimiyar gwamnati a kasar, tare da dawo da gwamnatin Abd Rabbuh Mansour Hadi wadda take kawar Riyadh.

Hadakar wadda Saudiyya ke jagoranta ta kasa cimma kowacce daga cikin manufofinta, a yayin da kuma dubunnan daruruwan mutanen kasar Yemen suka rasa rayukansu. Yemen a yanzu haka tana fuskantar wani hali ne wanda ya ke daya daga cikin mafi munin yanayi da bil-adama suka samu kansu a duniya.

No comments

Powered by Blogger.