'Yan dabar siyasa sun kora 'yan jarida da ma'aikatan zabe da gatura a garin Abeokuta
'Yan dabar siyasa sun kawo tsaiko ga gudanar da zabe a mazaba ta 13 rumfar zabe ta 22 a Itori Odo, Abeokuta ta Kudu da ke babban birnin jihar Ogun, wato Abeokuta.
'Yan jarida da malaman zabe, wadanda su ne 'yan dabar suka nufo, dole suka gudu domin su samu su tsira.
Wani jami'in tsaron farin kaya ya yi yunkurin ya tsirar da akwatunan zabe guda biyu, to amma sai suka fi karfinsa suka kwace su suka kuma lalata su nan take.
An dai fara samun matsala ne bayan da wakilin jam'iyyar APC ya nuna kin amincewarsa sakamakon daukar hotuna da 'yan jarida ke yi a wurin.
Daya daga cikinsu ya ce an basu umarnin kada su bari wani ya dauki hoto ko bidiyo a wurin, duk kuma kokarin da aka yi na fahimtar da wakilin bai saurara ba.
Ana cikin haka, sai daya daga cikin 'yan dabar mai suna Taiwo ya farmaki wakilin jam'iyyar ADC, wanda ya yi niyyar shiga tsakani.
Taiwo ya watsa giya a furkar wakilin jam'iyyar ta ADC, daga bisani kuma 'yan dabar suka fara bullowa daga kowanne bangare da gatura suna kai hari ga malaman zabe da kuma kayan zabe.
A bayanan da aka tattara dai, APC ba ta taba yin nasara a rumfar zaben ba, PDP ce ke yin nasara a wurin.
Haka kuma wani mutum da ya fito daga bangaren, Oluseyi Funmi, yana yin takarar zama dan majalisar jiha a karkashin jam'iyyar AA.
Post a Comment