Header Ads

'Yan Boko Haram sama da dubu tare da iyalansu sun mika wuya - Hukumar tsaron Nijeriya


Marigayi Shekau na BH da dakarunsa

Cibiyar Tsaron Nijeriya ta bayyana cewa mayakan Boko Haram guda 1,332, ciki har da iyalansu sun mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai cikin mako biyu da suka gabata a fadin arewa maso gabas. 

Manjo Janar Musa Danmadami, wanda shi ne daraktan harkokin yada labaran tsaro, ya bayyana haka, inda ya ce tsagerun na Boko Haram da suka mika wuya sun kunshi magidanta 222, mata 411 da kananan yara 699.

Daraktan ya bayyana cewa suna cigaba da tantance daruruwan mayakan da suka mika wuyan kafin daga bisani su dauki mataki na gaba a kan su, inda ya bayyana cewa sun kubutar da fararen hula 19, sun kashe wasu da ya kira 'yan ta'adda 8 tare da kuma wasu mutane 35 da suke zargi masu kai masu kayan bukatar rayuwa ne.

Kamar yadda Cibiyar Tsaron ta bayyana a jiya Alhamis a yayin taron ta da manema labaru duk bayan mako biyu, ta ma bayyana cewa sun ma karbi makamai daga mayakan, ciki harda AK-47 guda 14 da harsasan AK47 da bindigogin toka guda 2, gurneti 36, karamar bindigar mashinga 1 da daruruwan alburusan bindigar ta Mashinga.

Kamar yadda daraktan ya bayyana, a cikin mako biyu da suka gabata an kashe mayakan da dama ta hanyar jerin hare-haren jiragen sama tare da lalata harkokin ta'addancin su, inda ya kara da cewa duk kayan da sojoji suka gano, mutanen da suka kubutar da kuma mutanen da suka kama suna zargin mayakan ne duk sun mika su hukumomin da suka dace domin daukar mataki na gaba. 

Kamar yadda Janar din ya bayyana, manufar rage kashe takardun kudi ta Babban Bankin Nijeriya da kokarin da sojoji ke cigaba da yi sun taimaka wajen rage satar mutane domin neman kudin fansa.

Suma dakarun aikin Hadarin Daji da ke arewa maso yammacin Nijeriya sun samu nasarori da yawa ciki har da kashe 'yan fashin daji 13, kubutar da fararen hula 23. Sojoji kuma sun kwace bindigogin AK47 guda 7, harsasan bindigar 13 da kurtun harsasai masu yawa.

No comments

Powered by Blogger.