'Yan bindiga sun sace ma'aikatan zabe 19 tare da tafiya da kayan zabe
An sace ma'aikatan wucin gadi na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) mutum 19 da sanyin safiyar Asabar a jihar Imo.
Ma'aikatan na kan hanyar su ne ta zuwa rumfunan zabe daban-daban guda bakwai da ke mazabar Ugbelie mai lamba 06 da ke karamar hukumar Ideato South a jihar Imo a lokacin da aka sace su.
Hukumomin 'yan sanda a jihar ta Imo sun bayyana cewa an samu ceto duka ma'aikatan guda 19, a yayin da kakakin hukumar zabe ta INEC, Chinenye Chijioke-Osuji, ta tabbatar da afkuwar al'amarin.
Kakakin hukumar ta bayyana cewa an ceto ma'aikatan ne a yayin da aka yi kiran neman agajin gaggawa tare da yin bayani a kan al'amarin, inda su kuma jami'an tsaro suka fara aiki kan lamarin nan take.
An samu ceto ma'aikatan, sai dai Chinenye ta tabbatar da cewa duka kayan zaben wadanda suka hada da na'urar BVAS da sauran muhimman abubuwa ba a samu an karbe su ba.
Post a Comment