Header Ads

Yahudawa da dama na neman hanyar ficewa daga Isra'ila - Rahoto

Cincirindon Yahudawan da ne barin Isra'ila a iyafot

Sakamakon hatsarin da ke fuskantar kasar Isra'ila na siyasa da kuma dorewar ta a karkashin jagorancin firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, mutane da dama na neman hanyar ficewa daga kasar kamar yadda wata kafar watsa labaru ta Isra'ila ta bayyana. 

Jaridar mai amfani da yaren Hebrew mai suna Yedioth Ahronoth, ta bayyana a ranar Talata cewa mutane da dama na neman mafaka a kasashen waje sakamakon zanga-zangar da ake cigaba da yi a kasar ta Isra'ila biyo bayan yunkurin Benjamin Netanyahu na kwace ikon bangaren shari'a. 

"Yawan mutanen da ke naman su kasance 'yan wata kasa ya karu sosai." Kamar yadda jaridar da ke fitowa a Isra'ila kullum ta bayyana.

"Sakamakon abubuwan da ke faruwa a Isra'ila a 'yan kwanakin nan da kuma tunanin makomar ta a nan gaba, mun ga karuwar mutane masu neman kasancewa 'yan wasu kasashe da ke sassan duniya daban-daban."

Jaridar, wadda ta nakalto wani jawabi na lauyoyi da ke cikin jami'an shige-da-fici a Isra'ilan, ta bayyana cewa sun ce, "Muna fuskantar yawan wannan al'amari ta yadda yawan mutanen ba wai ya karu ne da kashi goma ba, a'a, sai dai da kashi dari in an kwatanta da baya. Kowanne lauya na karbar izinin neman zama dan wata kasa sau biyar ko shida a rana." 

Jaridar ta Yedioth Ahronoth ta bayyana cewa mutanen da ke neman zama 'yan wata kasar ba wai kawai cikin wadanda ba su goyon bayan shirin yin canje-canjen na Netanyahu ba ne, wadanda ma suke goyon bayan ya yi canje-canje a bangaren shari'ar su ma an gan su a cikinsu.

A cikin wani rahoton kuma, jaridar ta Isra'ila ta yi gargadin cewa masu kawo ziyara da 'yan yawon bude ido suma suna soke tafiye-tafiyen su zuwa yankunan da aka mamaye din sakamakon babbar zanga-zangar da ake yi kan yunkurin yin canje-canje ga sashen shari'ar na tsawon watanni biyu.

A dai ranar Litinin ne firaministan na Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa zai dakatar da kudurin yin canje-canjen ga sashen shari'ar kasar har sai wata mai zuwa, amma ya bayyana yana nan kudurinsa na yin canje-canjen.

No comments

Powered by Blogger.