Yadda za ku bibiyi sakamakon zaben shekarar 2023 da wayoyin hannayenku
Saboda sakamako ya fara fitowa na zabukan shekarar 2023 da aka gudanar, ga yadda za ku bi mataki-zuwa-mataki na yadda za ku bibiyi yadda abubuwan ke gudana ta hanyar amfani da wayoyin hannunku kuna zaune a gida.
1. A ziyarci shafin duba sakamakon zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC)
Domin hada akawunt, masu farawa a yanzu dole sai sun ziyarci shafin duba zabe na hukumar INEC wato http://inecelectionresults.ng.
2. Bayan an shiga, sai a danna "Creat Account" wato hada sabon shafi
Domin samar da shafin ka, sai a danna "Creat Account" wanda ya ke a shafin hukumar.
3. Ka rubuta bayanai da suka shafe ka
Ka rubuta bayanai da suka shafe ka, misali suna, adireshin imel, lamabar waya da lambobin sirri (password).
4. Tabbatar da adireshin imel da ake amfani da shi
Bayan sanya bayanan da suka shafe ka, za a turo maka da wasu lambobi domin tabbatar da adireshin imel din naka ta adireshin imel din da ka bayar. Bude imel din ka sai ka kwafi lambobin.
5. Ka shigar da lambobin da aka turo maka din
Dawo shafin hukumar ta INEC na duba sakamakon zabe domin sanya wadannan lambobi da aka turo maka ta adireshin imel.
6. Kammala hada shafin ka
Idan an tabbatar da lambobin da ka sanya, to sai ka kammala hada shafin ka ta hanyar samar da karin bayanan ka, kamar jihar ka ta asali, kwanan wata da aka haife ka, namiji ne ko mace.
7. Shiga cikin shafin da ka hada.
Bayan kammala duk matakan yin shafin na ka, sai ka shiga cikin shafin ta hanyar sa adireshin imel din ka da lambobin sirri (password).
A KULA DA WANNAN: In an bi wadannan matakai, za a iya bude shafi domin shiga shafin duba sakamakon zabe na hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta domin kallon yadda sakamakon zabe ya ke a yanzu. Yana da kyau a yi amfani da lambobin sirri (password) wadanda za a iya tunawa nan-da-nan kuma wadanda wani ba zai iya yin amfani da su ba.
Post a Comment