Header Ads

Yadda wasu Gwamnoni 8 suka yi tazarce a kan mukamansu

A Nijeriya, a ranar Asabar,18 ga watan Maci na shekarar 2023, aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jiha.

A yayin da an kammala tattarawa da fadin sakamakon zaben a wasu jihohi, wasu jihohin kuma ana cigaba da tattarawa.

Kawo yanzu, wasu gwamnoni da suka zarce a kan mukaminsu a wasu jihohi takwas sune:

Inuwa Yahaya na jihar Gombe

A jihar Gombe, hukumar zabe ta hannun jami'a mai tattara sakamakon zaben gwamna a jihar, Farfesa Maimuna Waziri, ta bayyana gwamnan jihar, Inuwa Yahaya, a matsayin wanda ya yi nasara ta sake darewa kan mukaminsa da kuri'u 345,821.


Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas

Farfesa Adenike Tamidayo Oladije, wanda shine babban jami'in tattara sakamakon zabe a jihar, ya bayyana gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, a matsayin wanda ya samu nasarar komawa kan mulki karo na biyu. 

Babajide Sanwo-Olu ya yi nasara ne da kuri'u 762,134.


Mai Mala Buni na jihar Yobe 

Shima gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya samu komawa kan kujerar mulki inda ya yi nasara da kuri'u 317,113 inda ya yi nasara kan babban abokin takararsa, Sheriff Abdullahi na jam'iyyar PDP wanda shi kuma ya samu kuri'u 104,259.


AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, shima ya samu nasarar kara komawa kan kujerar mulki a jihar Kwara.

Gwamnan AbdulRahman ya samu nasara a duka kananan hukumomin jihar ta Kwara.


Bala Muhammad na jihar Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, shima ya yi nasarar sake komawa kan kujerar mulki a jihar Bauchi da kuri'u 525,280 kamar yadda Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, jami'in tattara sakamakon zabe a jihar ya bayyana.

Babban abokin takarar gwamna Bala Muhammad shine Air Marshal Abubakar Sadique Baba wanda shi kuma ya samu kuri'u 432,272. 


Dapo Abiodun na jihar Ogun

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, shima ya zarca a kan mukaminsa a zaben gwamna da aka gudanar a jihar a ranar Asabar.

Gwamnan ya yi nasara ne da kuri'u 276,298, a yayin da babban abokin takararsa, Ladi Adebutu, na jam'iyyar PDP, ya samu kuri'u 262,383.


Seyi Makinde na jihar Oyo

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, na jam'iyyar PDP shima ya samu nasara a zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar a kan babban abokin takararsa, Teslim Folarin, na jam'iyyar APC da tazarar kuri'u kusan dubu 300. 


Abdullahi Sule na jihar Nasarawa 

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, shima ya yi nasarar zarcewa a kan mukamin nasa a zaben da aka gudanar, kamar yadda Ishaya Tanko, babban jami'in tattara sakamakon zabe a jihar bayyana.

Gwamnan ya samu nasara ne da kuri'u 347,209.

No comments

Powered by Blogger.