YADDA AKA YI JANA'IZAR SHAHIDAI 6 DA ELRUFA'I YA KASHE A KADUNA
A ranar Juma'a 17/03/23 da misalin karfe 12:00nr aka gabatar da Jana'izar Shahidai mutum shida wadanda Gwamnan Kaduna Nasiru elRufai ya sa aka harba a gabansa, wadanda suka yi shahada jiya a wurin muzaharar neman a bai wa Shaikh Zakzaky 'passport' dinsa domin neman lafiyar sa.
Jana'izar dai ta wakana a Fudiyya Rimi, Hayin Rigasa Kaduna, inda aka yi jana'izar ta Shahidai guda hudu, sannan a unguwar Badiko aka yi na mutum biyu. Bayan kammalawa an tafi da Shahidan Darur Rahma.
Post a Comment