Header Ads

Wata guguwa mai ƙarfin gaske ta hallaka mutane 25 tare da lalata dukiya mai yawa a Amurka

Wani gida da wata mota wadanda guguwar ta yi sanadiyyar lalatawa

Akalla mutane 25 suka rasu wasu da dama suka jikkata yayin da wata guguwa mai karfin gaske ta faru a jihar Mississippi da ke kudancin kasar Amurka, inda guguwar ta kware rufin gidaje, ta lalata motoci tare da rushe unguwanni baki daya. 

Guguwar, wadda ta ke hade da tsawa da ruwan sama, ta yi tafiyar sama da mil 100 (kilomita 60) a cikin jihar inda ta keta cikin garuruwa da dama da ke kan hanyar ta.

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Mississippi ta bayyana cewa mutane 25 suka rasu, da dama sun jikkata kuma mutane hudu da aka bayyana cewa ba a gan su ba, an gan su yanzu. 

A jihar Alabama, ofishin Sheriff da ke Morgan County ya bayyana a shafin sa na Twitter cewa mutum daya ne ya rasu a yayin da wata motar tirela ta juye da wani mutum yayin guguwar. 

A garin Rolling Fork kuwa, gidajen mutane kusan 2,000 suka rushe, motoci sun juye, katangu sun rushe kuma bishiyoyi sun fisgo daga kasa.

"Birni na ya tafi." Magajin garin Rolling Fork, Eldridge Walker, ya shaidawa CNN, "Rusassun abubuwa kawai na ke gani daga haguna zuwa damana."

"Za a runka jin abubuwan da aka rasa a garuruwan nan a jiki har abada." Gwamnan jihar Mississippi, Tate Reeves, ya bayyana a shafinsa na Twitter, "Ina rokon ku ku yi addu'ar samun taimakon Allah ga wadanda suka rasa iyalansu da abokanansu." 

Shi kuwa shugaban kasar Amurka, Joe Biden, bayyana hotunan da ke fitowa daga Mississippi ya yi da "masu sa karayar zuciya." Inda ya kara da cewa, "Za mu yi duk abinda ya kamata domin mu taimaka. Za mu kasance a wurin har sai abinda hali ya yi."

Irin wannan guguwa mai karfin gaske, wadda aka fi sani da Tornado a turance kuma wadda ta na da wahalar a iya yin hasashen ta, ta kan afku akai-akai a Amurka musamman a tsakiya da kuma kudancin kasar.

A cikin watan Janairu ma, iskar ta afku daya bayan daya a lokaci guda inda mutane da dama suka rasa rayukansu a jihohin Alabama da Georgia.

No comments

Powered by Blogger.