Header Ads

Wasu mutane na shirin tayar da hankali a lokacin zaben gwamnoni - Hukumar DSS


Wasu jami'an tsaron kasar nan 

Hukumar 'yan sandan ciki ta DSS ta bayyana cewa akwai shirin da wasu mutane ke yi na tayar da hankali a wasu sassan kasar nan yayin zaben gwamnoni da ke karatowa.

Kamar yadda ya ke a cikin wata sanarwa wadda mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya, ya fitar a ranar Laraba, hukumar ta yi gargadi ga mutane ko kungiyoyi da su guji yin abinda zai tayar da hankali domin kaucewa fushin hukuma. 

Hukumar sai ta yi kira ga 'yan siyasa da su kasance masu bin doka da oda a daidai lokacin da 'yan Nijeriya ke shirin fita rumfunan zabe domin zaben gwamnoni da 'yan majalisar dokoki a ranar 18 ga watan Maris.

Hukumar ta bayyana cewa ta shirya domin kare 'yan kasar wadanda ke da niyyar fita kada kuri'a kuma ta shirya tsaf tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro wajen dakile duk wani yunkuri na kawo rikici a lokacin zabukan.

No comments

Powered by Blogger.