Header Ads

Wasu gungun matasa sun sa wuta a wata kotu da ke jihar Ebonyi

Yadda cikin babbar kotun ya kone

Wasu gungun matasa da ake zargin 'yan dabar siyasa ne da yammacin ranar Talata sun afka cikin wata babbar kotu a da ke garin Owutu-Edda, karamar hukumar Afikpo ta Kudu da ke jihar Ebonyi tare da kunna mata wuta.

Rijistar kotun, Misis Oluchi Uduma, ta tabbatar da faruwar al'amarin a ranar Talata ga manema labaru a garin Owutu-Edda.

Kamar yadda ta bayyana, gungun mutanen sun afka cikin kotun ne a ranar Talata tare da sa ma ginin kotun wuta, kuma kundin takardun da ke cikin kotun da abubuwa masu muhimmanci duk sun kone baki daya.

Shugaban karamar hukumar ta Afikpo ta Kudu, Mista Chima Nkama, shima ya tabbatar da faruwar al'amarin, inda ya ce an sanar da wannan al'amari ga 'yan sanda.

No comments

Powered by Blogger.