Wannan shi ne zaben shugaban kasa mafi muni, zan kalubalance shi a kotu - Alhaji Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana zaben shugaban kasar da aka gudanar a Nijeriya da mafi muni, inda ya bayyana cewa zai kalubalance shi a kotu.
Dan takarar, wanda ke magana a yayin wani taro da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis, ya sha alwashin zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben wanda ya yi imanin cewa an murguda shi domin APC ta yi nasara.
Ya dai tabbatar da cewa matsayarsa ta cewa zaben na cike da magudi masu sa idon cikin gida da na sauran kasashen waje za su iya tabbatar da hakan.
Atiku Abubakar, wanda ya bayyana cewa lokaci bai kurewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin abinda ya kamata ya yi ba, ya bayyana cewa zaben na ranar Asabar da ya gabata ya shafi makomar matasa, inda ya tabbatar da cewa zai cigaba da gwagwarmaya domin tabbatar da damakaradiyya da samun kyakkyawar makoma ga matasa.
"Nijeriya ce fatar Afirka da kuma duniya. Fata na shine bangaren shari'a ya yunkura ya yi abinda ya kamata ya yi a wannan lokacin. Ina kira ga duka mutanen kwarai maza da mata da su zo mu hada hannu domin samar da kariya ga tsarin mulkin Nijeriya.
"Ina son 'yan Nijeriya su dage su kuma kasance masu sadaukarwa. Ba za mu zauna mu sa ido muna kallo a kwace hakkokinku daga wurin ku ba. Za a saurari muryoyin ku."
Post a Comment