Wani soja ya kashe wani babban kwamandan sojoji a jihar Sokoto
Wani sojan Nijeriya, Lance Corporal Nwobodo Chinoso, ya kashe wani babban kwamandan sojojin a Rabah da ke jihar Sokoto, Lt. Sam Oladapo.
A yayin wannan harbi da sojan yayi wanda ya afku a karshen mako, Chinoso bayan ya kashe Oladipo, ya ma harbi wani sojan mai suna Sajent Iliyasu da kuma wani sojan mai karamin matsayi, Firabet Attahiru Mohammed.
Bayan kuma ya harbi wadannan sojoji, kamar yadda kafar watsa labaru ta PRNigeria ta ruwaito, shima sai ya harbe kansa har lahira.
Majiyoyi masu karfi da aka tuntuba a Sokoto sun kasa yin bayanin yadda kwakwalwar sojan da ya yi harbin take, sai dai wani daga cikin sojojin ya shaidaya PRNIgeria cewa: "A lokacin da al'amarin ya faru, kwamandan sashi na 8 na nan kuma kwamandan runduna ta 26 duk suna wannan waje. Sun yi kokarin kai gawawwakin sojojin asibitin Usmanu Dan Fodio, duk da cewa sun bada umarnin a gudanar da bincike cikin al'amarin."
A yayin da ya ke jawabi ba tare da bukatar a bayyana shi ba, wani babban soja da ke Sokoto ya fadawa PRNigeria cewa, "Sojan da ya kashe kwamandansa da kuma wasu abokan aikinsa guda biyu, ta yiwu yana fama da matsalolin yanayin aiki ne da wadanda suka shafi kwakwalwa.
"Wani abu ne da jami'an soja suka saba yi. To amma wannan ba hujja ba ce ga kowanne soja ya yi hakan. Tabbas, za a dauki kwakkwaran mataki domin hana faruwar hakan a nan gaba."
Post a Comment