Header Ads

Wani minista a Isra'ila ya bukaci a "kawar" da wani kauye na Palasdinawa


Hoton wani wurin sai da motoci da aka sa wa wuta a garin Huwara da ke kusa da Nablus a yankin yamma da gabar kogin Jordan da aka mamaye.

Wani babban minista a kasar Isara'ila ya bukaci a kawar da wani kauye na Falasdinawa kwanaki kadan bayan 'yan Isra'ila da ke zaune ba kan ka'ida ba sun kawo hare-hare a kauyen wanda ke kusa da Nablus a yankin yamma da gabar kogin Jordan wanda aka mamaye.

"Ina tunanin ya kamata a kawar da Huwara." Kamar yadda ministan kudi na Isra'ila, Bezelel Smotrich, wanda kuma ya ke kula da sha'anin da ya shafi fararen hula a yankin da aka mamaye na yamma da kogin Jordan ya bayyana, "Isra'ila ya kamata ta yi hakan." Kamar yadda kafar watsa labarun Isra'ila ta ruwaito a ranar Laraba.

A cikin daren ranar Lahadi, daruruwan mazauna 'yan Isra'ila suka kai hari a Huwara da wasu kauyuka da ke zageye da shi inda suka sa wuta a motoci da gidaje masu yawa. Abinda ya harzuka su shine kashe wasu 'yan uwan juna biyu da wani bafalasdine mai dauke da bindiga ya yi a kauyen Huwara.

Mutum daya daga Falasdinawa ya rasa ransa a yayin da sama da mutane 390 suka jikkata, inda kafofin watsa labarun Falasdinawa suka bayyana cewa wadanda suka kawo harin sun yi sara da karafuna da duwatsu.

Kungiyoyin kare hakkin bil-adama da ke Isra'ila, Peace Now da kuma B'Tselem, sun bayyana harin da mazauna 'yan Isra'ilan suka kai da "kisan kiyashi da aka tsara" wanda ya samu goyon baya daga gwamnatin mamaya.

Hare-hare a kan Falasdinawa na ta kara karuwa tun bayan da Benjamin Netanyahu ya sake dawowa a matsayin Firaminista cikin watan Disambar shekarar da ta gabata.

Sojojin Isra'ila sun kai manyan hare-hare har guda uku bayan da sabuwar majalisar kasar ta fara aiki, na bayan nan a cikin watan da ya gabata a Nablus wanda ya haifar da kisa wanda sojoji suka yiwa Falasdinawa mafi yawa tun bayan shekarar 2015.

Firaministan Falasdinawa, Mohammad Shtayyeh, ya yi kira da "shigowar kasashen duniya" domin kawo karshen laifuffukan Isra'ila.

"Mun dora alhakin wadannan laifuffuka a kan gwamnatin mamayar, wannan na yin nuni ne da irin shirye-shirye wanda gwamnatin Isra'ila ke yi, wadda Minsitocinta ke goyon bayan laifuffuka da suka sabawa dokokin duniya." Kamar yadda ya bayyana a cikin wani jawabi a ranar Litinin.

No comments

Powered by Blogger.