Wani matashi ya kashe wani dalibi da wuka a jihar Zamfara
Wani matashi a garin Talatar Mafara da ke jihar Zamfara ya kashe wani dalibi mai suna Imamu ta hanyar caka masa wuka a makogwaronsa, sanadiyyar haka kuma ya rasu.
Al'amarin ya faru ne a safiyar Talata 15 ga watan Sha'aban shekara ta 1,444 wato daidai da 7 ga watan Maris shekarar 2023.
Marigayin mai suna Imamu, da ne ga shugaban makarantar Fudiyya Nursery and Primary da ke garin Talatar Mafara mai suna Malam Sanusi Ahmad Wadata.
Wanda ya aikata laifin ya gudu a yayin da shi kuma marigayin ya rasu nan take, to amma an san mahaifansa.
Marigayin dalibi ne na Fudiyya kuma mai kwazo, mahaifinsa kuma koyarwa yake yi kuma mai kokari a cikin harka Islamiyya karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H), yayin da 'ya'yansa kuma yara ne masu tarbiyya ta addini.
Allah ya gafarta masa ya kuma ba mahaifansa da sauran musulmi hakurin rashin.
Post a Comment