Ƙungiyar IPOB ta shiga cikin jerin ƙungiyoyin ta'adda 20 mafi hatsari a duniya - Rahoto
Kungiyar nan wadda ba kan ka'ida ta ke ba ta masu fafutikar kafa kasar Biyafara (IPOB) ta shiga cikin jerin kungiyoyin ta'adda 20 mafi hatsari a duniya, duk da cewa al'amarin ta'addanci na kara raguwa a Nijeriya, kamar yadda 2023 Global Terrorism Index (GTI) ya bayyana.
Yanzu Nijeriya ita ce ta takwas a duniya cikin kasashen da suka fuskanci kalubale sakamakon ayyukan ta'addanci a cikin shekarar 2022, kamar yadda rahoton ya nuna.
Afghanistan, a cikin shekaru hudu ta kasance kasar da tafi kowacce kasa fuskantar kalubale sakamakon ayyukan ta'addanci, sai kasashen Afirka uku da ke bi mata na Burkina Faso (ta biyu), Somaliya (ta uku), Mali (ta hudu).
Kasar Siriya ta biyar a cikin jerin, Pakistan ta shida sai Iraki ta bakwai.
Bayan Nijeriya, Myanmar (Burma) ta zo ta tara a yayin da makwafciyar Nijeriya, Nijer, ta zo ta goma a cikin jerin kasashen da suka fuskanci kalubale mai karfi sakamakon ta'addanci a shekarar 2022.
Rahoton na GTI wanda aka fitar a ranar Talata shine karo na 10. Rahoton na bin diddikin ta'addanci ne a fadin duniya, kuma cibiyar Institute for Economics and Peace ce ke samar da shi, wadda tana zaman kan ta ne, ba tare da neman riba ba kuma ba mai nuna bangaranci ba, wadda ke Sydney kasar Australia.
Rahoton na GTI ya sa kungiyar IPOB a matsayin ta 10 a cikin 20 na kungiyoyin ta'addanci mafi hatsari a duniya, a yayin da Islamic State, wadda ke ayyukanta a yankunan kasashen Iraki da Siriya ta zo ta daya a jerin.
Islamic State West Africa (ISWA) wadda ta zo na shida a duniya, ta zo ta daya a matsayin kungiyar da ta fi kowacce hadari a Nijeriya, inda Boko Haram ke bi mata, wadda ita kuma ta zo ta bakwai a duniya.
"Kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biyafara (IPOB) wadda gwamnatin Nijeriya ta bayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda a cikin shekarar 2017, shekarar 2022 ta kasance shekarar da ayyukanta suka fi muni. Su ne ke da alhakin hare-hare har 40 da kuma mutuwar mutane 57 a shekarar 2022, wanda hakan ke nuna karuwar hare-hare daga 26 da kuma mutuwar mutane 34 a shekarar da ta gabata." Kamar yadda rahoton ya nuna.
Kungiyar ta IPOB na fafutikar kafa kasar Biyafara ne wadda ta ke son fitarwa daga yankin masu amfani da yaren Inyamuranci na kudu-maso-gabas da kuma wani bangare na yankin kudu-maso-kudu na Nijeriya.
Rahoton shekarar da ta gabata na GTI din ya ta'allaka yawan hare-hare a kan 'yan sanda da kuma sauran jami'an tsaro a Nijeriya kan yawan arangama a tsakanin jami'an tsaro da mambobin kungiyar ta IPOB.
"Jami'an tsaro, wadanda suka hada da 'yan sanda da ma'aikatan kurkuku sun kasance wadanda suka fi samun hare-hare fiye da sojoji da kuma fararen hula a shekarar 2022. Hare-hare a kan 'yan sanda da kuma jami'an gidan kurkuku ya karu daga 1 a cikin shekarar 2020 zuwa 75 a cikin shekarar 2021, wanda ya wuce kashi uku na duka hare-haren da aka kai a Nijeriya a cikin shekarar 2021.
"Hakan ya afku ne sakamakon hauhawar arangama a tsakanin jami'an tsaro da kuma mambobin kungiyar masu neman su ware, kamar kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biyafara (IPOB)."
Shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, a yanzu haka yana Abuja inda ake tsare da shi.
Rahoton ya bayyana cewa yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon ayyukan ta'addanci ya ragu, hare-hare da kungiyar ISWA da kuma na Boko Haram ke kaiwa suma sun ragu.
Harin ta'addanci mafi muni wanda aka yi a Nijeriya a shekarar 2022 shine wanda aka kai a ranar 22 ga watan Mayu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 50. ISWA wadda itace ta daukin nauyin harin ta bayyana cewa wadanda abin ya shafa suna bibiyarta ne kuma suna kai bayananta ga hukumomin tsaro.
Post a Comment