Header Ads

Tsawa ta yi sanadiyyar rasuwar mutane 23 a gabashin India

Akalla mutane 23 ne suka rasa ransu sakamakon tsawa da aka yi yayin wata iska da aka yi mai karfi a gabashin kasar India, kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Rasa rayukan da aka yi a jihar Bihar da ke India din sun afku ne a tsakanin ranakun Laraba da Juma'a, wadanda abin ya fi shafa kuwa manoma ne da 'yan kwadago.

Babban Minista da ke Bihar, Nitish Kumar, ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa sakamakon rasa rayukan tare da shan alwashin biyan su diyya.

Mutane 11 ne dai suka mutu a wurare da dama na jihar a ranar Juma'a bayan mutane 13 da suka rasu kwanaki biyu kafin nan, kamar yadda hukumar kula da anoba ta jihar Bihar ta yi kididdiga. 

Ana hasashen kara samun ruwan sama mai karfi da tsawa a yankunan jihar a ranar Litinin.

Tsawa mai karfi dai an saba ganinta ne a kasar India a tsakanin watannin Yuni da Satumba, hakan na sake kyautata samuwar ruwa to amma ya kan kasance sanadin lalacewar abubuwa da dama da kuma mace-mace a kowacce shekara.

Kusan mutane 2,900 tsawa ta kashe a India a cikin shekarar 2019, kamar yadda National Crime Records Bureau a India ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.