Header Ads

Tinubu ya kafa kwamitin sasantawa da Atiku da Obi


Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi, zababben shugaban kasa, Ahmed Bola Tinubu da kuma na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar

Zababben shugaban kasar Nijeriya, Ahmed Bola Tinubu, ya kafa kwamiti domin haduwa da sauran 'yan takarar kujerar shugaban kasa na sauran jam'iyyu.

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ne ya bayyana haka a ranar Talata a Abuja a yayin da zababben shugaban kasar, Ahmed Bola Tinubu, da zababben mataimakinsa, Kashim Shetima, suke karbar shaidar lashe zaben na shugaban kasa, inda ya kara da cewa a cikin kwamitin akwai dattijai daga jam'iyyar APC.

A cikin wani jawabi wanda mataimakin gwamnan a bangaren 'yan jaridu, Richard Olatunde, ya sawa hannu,
Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa shima yana daya daga cikin kwamitin, inda ya kara da cewa suna so su hadu da sauran 'yan takarar ne domin su lallashe su a yi aiki tare kuma duk wani wanda ke da korafi za a hadu da shi domin sasantawa.

Ya bayyana cewa kuri'u da jam'iyyar APC ta samu a jihar Ondo na nuni da yadda mutane ke son mulkinsa ne, inda ya ce mutane sun goyi bayansa na ganin an samu shugaban kasa wanda ya fito daga kudancin kasa, sun sa duka karfinsu kuma shi ya sa suka yi nasara.

"Wannan zabe ne wanda ba a cika masa abubuwan da za su kasance marasa amfani ba. Mutanen da suka yi zabe an kirga su, a haka na ke kallon zaben ba wai wanda ya ke nuni da miliyoyin kuri'u ba kawai. In kun lura, cikin 'yan takarar kowa ya samu jihohi 12, ba a taba haka ba a da." Ya bayyana.

A zaben na shugaban kasa da aka kammala, zababben shugaban kasar, Ahmed Bola Tinubu, ya samu kuri'u 8,794,726 ne inda ya yi nasara a kan Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, wanda ya samu kuri'u 6,984,520 da kuma Peter Obi na jam'iyyar LP (Labour Party) wanda ya samu kuri'u 6,101,533.

No comments

Powered by Blogger.