TALBA TA LASHE ZABEN 'YAR MAJALISA MAI WAKILTAR NANGERE/POTISKUM A YOBE
Daga Yusuf Waliy
An bayyana Hajiya Fatima Talba ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen Nangere Potiskum a majalisar Wakilai ta ƙasa bayan ta cika sharuddan doka ta hanyar samun ƙuri’u mafi rinjaye na ƙuri’u 36,407.
Jami’in Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta Farfesa Bashir O. Bello ne ya sanar da hakan da daren jiya Laraba a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke cikin Makarantar CAMTECH Potiskum, jihar Yobe.
A cewar sa, ‘yan takarar jam’iyyu daban-daban ne suka fafata a zaɓen kamar haka; Ɗan takarar AA Sulayman Lampo Abubakar ya samu ƙuri’u 437, Adamu Musa na ADC ya samu 546 ya yin da Fatima Talba ta APC ta samu ƙuri’u 36,407.
Sauran sun haɗa da Ali Yakubu NNPP 2,744, Adamu Abubakar Waziri na PDP 36,097 da Iliya Mohammed Maina Kaina na YPP 391.
Wannan shi ne Karo na biyu da ake zaɓar Hajiya Talba, a matsayin 'yar majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar Nangere/Potiskum.
Post a Comment