Ta'addanci: Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da mataimakan Sheikh Gumi, Mamu, a kotu
Gwamnatin Nijeriya a ranar Talata, 21 ga watan Maci shekarar 2023, ta gurfanar da Malam Tukur Mamu, wanda ya ke sasantawa da 'yan ta'adda kuma mataimaki ga Sheikh Ahmad Gumi, a kotu a kan caje-caje har guda goma da suka shafi samar da kudi ga ta'addanci da sauransu.
Mamu, wanda ofishin Antoni Janar na Nijeriya ne ke yin shari'a da shi, za a gurfanar da shi a gaban alkalin babbar kotun tarayya ne da ke Abuja, Alkali Iyang Ekwo.
Dama ko kafin nan, Alkali Nkeonye Maha, a ranar 13 ga watan Satumbar shekarar 2022, ya taba bayar da umarni ga hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) da su kamo shi su tsare shi har tsawon kwana 60.
Wannan kuwa, kamar yadda kotun ta bayyana, domin hukumar DSS din ta samu ta kammala binciken ta ne a kan Mamu din, wanda ya jagoranci sasantawa da 'yan ta'adda domin sako fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Legas da aka yi garkuwa da su a watan Macin shekarar 2022.
Daraktan shigar da caje-caje na kasa, M.B Abubakar ne ya sa hannu a cajin.
Post a Comment