Header Ads

Sojojin Saudiyya sun kama wata 'yar fafutika yayin da take yin Umura

Rania Al-assal

Jami'an tsaron Saudiyya sun kama wata fitacciyar 'yar jarida 'yar fafutika wadda ke kasar Misra a birnin Makkah a yayin da ta ke gudanar da Umara a yayin da gidan sarautar ta Saud ke amfani da kame domin dakatar da muryoyin da ba su yi masu daidai ba.

Mutane da dama a cikin rubuce-rubuce da dama a shafin sada zumunta na Twitter sun bayyana cewa Rania al-Assal ta tafi kasar Saudi Arabiya kusan kwana 50 da suka wuce domin yin aikin umara. To sai dai ba a ji daga gare ta ba kuma ba a san inda ta ke ba. 

Masu fafutika da ke kafofin sada zumunta sun bayyana cewa al-Assal babbar mai goyon bayan fafutika ce kan Isra'ila kuma a gaba ta ke wajen fafutikar Falasdinawa da kasar Yemen, kuma a tsawon lokaci ta kasance tana kalubalantar irin siyasar Saudi Arabiya da Isra'ila a yankin yammacin gabas ta tsakiya. 

'Yar fafutikar ta dade tana kalubalantar irin abubuwan da Saudiyya ke yi a kasar Yemen, kuma akai-akai ta kan yi tir da yin kawanya ga kasar wadda yaki ya daidaita.

Masu fafutika na nuna damuwa kwarai a kan makomar Assal, kuma suna kira ga Saudi Arabiya da ta yi bayani a kan ina ta ke.

A cikin watan Fabrairu da ya gabata, jami'an tsaron na Saudiyya sun kama wata mata 'yar kasar Yemen, Marwa al-Sabri, a yayin da ta ke yin aikin umara.

Kwamitin matan kasar Yemen ta yi Allah wadai da kamen na ta a wancan lokaci, inda suka bayyana kamata din da karya dokokin bil-adama, mutuntaka, addini da tsari.

Kwamitin, a cikin wani jawabi wanda kafar watsa labarai ta kasar Yemen, Saba News Agency, ta samu, sun bayyana kama ta din da cigaba da musgunawa da Saudiyya ke yiwa kasar Yemen, cigaba da yaki a kan ta da kuma hana shiga ko fita cikin ta.

Sun bayyana cewa matar 'yar kasar Yemen an tsoratar da ita tare da fada mata kalamai masu cutarwa, inda suka yi kira ga masu fafutikar 'yancin bil-adama da sauran kungiyoyi da su yi Allah wadai da kamun na ta kuma su tursasawa Saudiyya sako ta tare da mayar da ita kasar Yemen.

Tun bayana zamowar Mohammed bin Salman yarima ga sarkin Saudiyya a cikin shekarar 2017, masarautar ta kame masu fafutika da dama, masu rubuce-rubuce, masana da duk wadanda ake ganin masu adawar siyasa ne ba tare da nuna mutuntawa ga banbancin ra'ayi ba duk da cewa kasashen duniya sun yi Allah wadai da irin wannan al'amari. 

A sakamakon haka an kashe malaman addinin musulunci, masu fafutika mata an sa su kurkuku, kuma an cigaba da hana 'yancin bayyana ra'ayi, kasancewa a wata kungiya da addini. 

A cikin shekarun baya, Riyadh ta yi canje-canje ga dokokin ta da suka shafi ta'addanci domin su hada da fafutika a ciki.

No comments

Powered by Blogger.