Header Ads

Sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasdine a ranar daya ga watan Ramadan

Marigayi Amir Imar Abu Khadijeh

Sojojin Isra'ila sun harba wani bafalasdine a ranar daya ga watan Ramadan yayin da suka zagaye gidansa tare da bincike a ciki a kauyen Izbat Shoufa, kudu-maso-gabashin birnin da ke gabar yamma na Tulkarm.

Mutumin dan shekara 25 mai suna Amir Imar Abu Khadijeh, an dauke shi zuwa asibiti bayan harsashe ya same shi a kai a ranar Alhamis.

Harbin ya haifar da yagewar kashin kansa, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta shaida, kuma an ma harba shi a kasan jikinsa.

Kamar yadda wani mai rajin kare hakki na kauyen, Murad Droubi, ya bayyana, wani gungun sojoji masu yawa ne suka afko kauyen, suka kulle hanyoyin shigarsa suka kuma hana mutane da motoci tafiya a cikin kauyen yayin da suka zagaye wani gida.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an ji harbin bindiga yayin da sojojin ke zagaye da wani gida wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar Abu Khadijeh.

Tun farkon wannan shekarar, akalla falasdinawa 90, ciki da yara 17 da mace 1, sojojin Isra'ila suka kashe kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta bayyana.

A cikin watannin da suka gabata, Isra'ila ta kara kaimi wajen kai hare-hare a kan garuruwa da biranen Falasdinawa a yankunan da ta mamaye. Sakamakon haka Falasdinawa da yawa sun rasa rayukansu kuma an kama da yawa.

Mafi yawancin irin wannan afkowa da sojojin ke yi sun fi yawa a Nablus da Jenin, inda sojojin Isra'ilan ke kokarin hana fafutika a biranen Falasdinawa da aka mamaye.

Kungiyoyin cikin gida da na duniya na kare hakkin bil-adama sun yi Allah wadai da amfani da karfi mara kima da Isra'ila ke yi da "tsarin harbi domin kisa" da ta ke amfani da shi a kan Falasdinawa.

No comments

Powered by Blogger.