Sojojin Isra'ila sun auka cikin masallacin Kudus tare da koro musulmi masu gabatar da ibada waje
An koro musulmai masu gabatar da ibada daga cikin masallacin Kudus a yayin da sojojin Isra'ila da wasu masu tsatstsauran ra'ayi suka afko cikin harabar masallacin a ranar da ake gabatar da azumin watan Ramadan na hudu.
A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna sojojin Isra'ila da wasu yahudawa 'yan kama-wuri-zauna masu tsatstsauran ra'ayi na korar musulman daga masallacin a ranar Lahadi.
Tawagar masu tsatstsauran ra'ayin, wadanda suka afko a ranar Lahadi, suna karkashin kulawar sojojin Isra'ila ne.
Kamar yadda Wafa News Agency ta bayyana, Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Falasdinawa, ta yi kira da a tilastawa Isra'ila bin ka'ida kuma "ta dakatar da keta hurumin wurare masu tsarki a Kudus, ciki har da masallacin Kudus, kafin lokaci ya kure."
Ma'aikatar ta bayyana hari a kan masu ibadar a matsayin "rikitar da yadda abubuwa ke tafiya" kuma ta bayyana Tel Aviv a matsayin wadda za ta kasance mai nauyin ko menene ya biyo baya.
A wajen musulmai, masallacin Kudus shine wuri mafi girma na uku.
An dai samu hargitsin ne bayan 'yan sandan Isra'ila sun amince da a afka cikin masallacin karkashin umarnin ministan Isra'ila, Itamar Ben Gvir.
A ranar Alhamis, daya ga watan Ramadan, sama da masu tsatstsauran ra'ayi 300 suka afka harabar masallacin.
Shugaban kwamitin addinin musulunci a masallacin kudus, Shaikh Ekrama Sabri, ya yi gargadi game da yin hari a masallacin, inda ya bayyana cewa sojojin na son cire masu ibadar ne daga masallacin domin samar da hanya ga yahudawa 'yan kama-wuri-zauna su afka masallacin tare domin yin hargitsi tare da keta alfarma.
Falasdinawa da yawa sun yi kira ga masu gabatar da ibadar da su runka shan ruwa a harabar masallacin bayan kai azuminsu kuma su runka yin sallah a masallacin.
Daya daga cikin dalilin Falasdinawan na yin hakan shi ne tabbatar kasancewarsu a masallacin kudus da nuna mallakar sa da kuma mallakar birnin Kudus, a yayin da yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ke cigaba da haifar da yamutsi.
A shekarun da suka gabata a kan samu arangama a tsakanin sojojin Isra'ila da Falasdinawa a lokacin azumin Ramadan, musamman a harabar masallacin Kudus, wanda shine wuri mafi daraja na uku a musulunci.
Post a Comment