Header Ads

Sojojin Isara'ila sun kashe wani Bafalasdine a yayin da hare-haren su ke kara hauhawa

Marigayi Omar Sawaed

Sojojin Isra'ila sun kara kashe wani matashin Bafalasdine a arewacin yankunan da ta mamaye a yayin da hare-haren ta ke kara hauhawa a gabakidaya fadin kasar Falasdinu da ta mamaye.

Bafalasdinen mai shekara 22, Omar Sawaed, an kashe shi ne a garin Kafr Yasif wanda Isra'ila ta mamaye tun cikin shekarar 1948 kamar yadda cibiyar bayanai ta falasdinawa ta bayyana a ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe shi ne lokacin da ya ke cikin wata mota kuma aka jefo shi waje daga cikin motar da ke tafiya inda ya samu mummunan rauni daga baya kuma aka bayyana cewa ya rasu.

A cikin wani al'amari mai kama da wannan, a ranar Alhamis, wani Bafalasdine dan shekara 25 mai suna Amir Imar Abu Khadijeh, shima sojojin Isra'ila sun harbe shi inda ya rasa ransa lokacin da suka zagaye gidansa da ke kauyen Izbat Shoufa da ke kudu-maso-gabashin birnin gabar yamma na Tulkarm. 

Gwamnatin Isra'ila ta kara lunka munanan hare-haren ta a watannin da suka gabata ga Falasdinawa a baki daya yankunan da ta mamaye. A sakamakon haka, Falasdinawa da yawa sun rasa rayukansu kuma an kame da yawa.

Sun fi yin hare-haren mafi yawanci a Jenin da Nablus, inda sojojin Isra'ilan ke kokarin hana kafuwar masu futikar Falasdinawa a biranen Falasdinawa. 

A wannan shekarar kawai, sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa kusan 90, mafi yawancinsu a yankin da aka mamaye na yamma da kogin Jordan. Wannan shekara ta fara da afkuwar munanan abubuwa ga Falasdinawan wannan yankin cikin kusan shekaru ishirin. 

Kungiyoyin kare hakkin bil-adama na cikin gida da kasashen waje sun yi Allah wadai da tsarin Isra'ila na "harbi domin kisa" a kan Falasdinawa.

No comments

Powered by Blogger.