Header Ads

Sojojin hadin gwiwa na kasa-da-kasa sun kama masu taimaka wa mayakan Boko Haram da ISWAP sama da 900

Sojojin hadin gwiwa na kasa-da-kasa (MNJTF) sun bayyana cewa a sakamakon yaki da suke yi da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da kuma hare-hare ta jiragen sama da kuma wasu ayyuka da suke gudanarwa a cikin kasa, mambobin kungiyoyin mayaka masu yawan gaske, su da iyalansu, suna ta barin dajin Sambisa suna tafiya kusa da Tafkin Chadi a cikin wata daya da ya gabata. 

A cikin wani jawabi da hadakar ta MNJTF ta fitar ranar Laraba ta bakin mai hulda da jama'a na sojojin na hadaka da ke birnin N'Djamena a kasar Chadi, Laftanar Kanar Kamarudeen Adegoke, hadakar ta bayyana cewa sojojinsu na bangare 3 da na 4 sun kama wadanda ake zargi iyalai ne da mataimakan Boko Haram da ISWAP sama da 900.

"Bayan haka sojoji da ke bangare na 4 su kuma a yayin da suke yin sintiri da dare a yankin Ngagam - Djalori sun ceto mata uku da yaransu hudu daga dajin Sambisa yayin da suke gudu daga fadan da ake yi tsakanin mayakan Boko Haram da na ISWAP a cikin dajin Sambisa.

"A ranar 8 ga watan Maci, sojojin Nijeriya da aka ajiye a Damasak sun ci karo da iyalan 'yan ta'addan su 70, mata 43 yara 30.

"A yanzu haka suna samun kulawar likitoci." Kamar yadda ya bayyana.

Wannan kuwa, kamar yadda ya ce, ya biyo bayan kama wasu da ake zargi masu hada kai da taimakawa 'yan Boko Haram da ISWAP din ne da dabaru, Muhammed Sabo da Sarki Danladi wadanda ke kokarin barin garin Munguno su tafi Tumbuns domin haduwa da 'yan ta'addan, da kuma wani mai suna Abubakar Usman wanda aka kama a ranar 5 ga watan Maci, wanda a yayin tambayoyin da aka fara yi ya tabbatar da cewa ya kan kai dabaru da dama ga 'yan ta'addan.

A yayin da ya ke jawabi a garesu, kwamandan sojojin, Mejo Janar AbdulKhalifa Ibrahim, ya yabawa sojojin da kwamandojinsu, inda ya bayyana cewa kada su sassauta wajen ganin sun hana 'yan Boko Haram din da mayakan ISWAP samun duk wani bayani ko dabaru, tare da cewa karshensu ya zo kusa, domin haka su kara kaimi tare da tabbatar da cewa za su samu taimako daga cibiyar ta MNJTF akai-akai.

Kwamandan ya yi kira ga mutanen da ke yankin Tafkin Chadi da su sa ido sosai su kuma kai rahoton duk wani abu mai alamar tambaya ga jami'an tsaro.

No comments

Powered by Blogger.