Header Ads

Siyasa ta zama gado: 'Ya'ya da matan 'yan siyasa da ke shirin shigewa majalisar wakilai ta kasa ta 10 wadda za a rantsar


Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai tare da dan sa, Bello Nasir El-Rufai

Yara da iyalan sanannun 'yan siyasa da masu mulki a Nijeriya sune za su mulki majalisar wakilai ta kasa ta 10 wadda za a rantsar a watan Yunin shekarar 2023.

A ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 'yan Nijeriya suka fara jefa kuri'a domin gabatar da zabe rukuni na farko na babban zaben shekarar 2023, tuni wadanda suka yi nasara a zabukan shugaban kasa, 'yan majalisun jaha da sanatoci suka fito. To sai dai yara da matan sanannun mutane, musamman 'yan siyasa, da yawa sun kasance su aka zaba a matsayin mambobin majalisar wakilai ta 10 da za a rantsar, wannan kuwa bai ma hada da wadanda ke takarar majalisar wakilai a jihohinsu ba. 

Bello (Nasir El-Rufai)

Bello, daya daga cikin 'ya 'yan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai kasance a cikin majalisar ta 10 mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa. Ya yi takara a karkashin jam'iyyar APC inda ya yi nasara a kan abokin takararsa Suleiman Abdu da kuri'u 51,052 inda abokin takarar ya samu kuri'u 34,808. Gwamnan ya kasance sananne a cikin kasa na wani lokaci. A yayin mulkin Olusegun Obasanjo, daga cikin mukaman da ya rike akwai darakta mai kula da saye-sayen abubuwa da ake yi a kasa, shine kuma sakataren majalisar kula da sayar da kayan gwamnati da ake yi a karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya jagoranci sayar da kadarorin gwamnati. Shi ne ma kuma ministan babban birnin tarayya a tsakanin shekarun 2003 da 2007. Shine gwamnan jihar Kaduna tun shekarar 2015 a karkashin jam'iyyar APC. Mulkin da ya yi karo biyu na shekara takwas zai kawo karshe ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023.


Abdulaziz (Umaru Yar'adua)

Kanine ga tsohon shugaban kasar Nijeriya, marigayi Umaru Yar'adua, shine zai wakilci yankin Katsina ta tsakiya a majalisar ta 10. Sunansa Abdulaziz Yar'adua, sojan kasa ne Laftanar kanar mai ritaya. Dan uwansa shine gwamnan jihar Katsina a tsakanin shekarun 1999 da 2007 kafin ya zama shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP. An bayyana cewa shine gwamna na farko da ya bayyana kadarorinsa ga kasa. Kamar yadda Wikipedia ta bayyana, a yayin mika mulkin soja na Ibrahim Babangida ga jamhuriya ta uku, Yar'adua na cikin wadanda suka samar da People Front of Nigeria, tare da shi akwai Atiku Abubakar, Babagana Kingibe, Bola Tinubu, Sabo Bakin Zuwo, Wada Abubakar, Abdullahi Aliyu Sumaila, Abubakar Koko da Rabiu Musa Kwankwaso, wadda kungiya ce ta siyasa a karkashin jagorancin dan uwansa marigayi Mejo Janar Shehu Musa Yar'adua. Wannan kungiyar daga baya sai ta koma jam'iyyar siyasa mai suna Social Democratic Party, wadda ta yi nasara a zaben shugaban kasa na watan Yunin shekarar 1993 inda MKO Abiola ne ya kasance dan takarar ta. 

Sadiq (Ango Abdullahi)

Shugaban majalisar dattawan arewa, ko tantama babu mutum ne mai jama'a. Tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya ma kasance shugaban kwamishinan tsara tattalin arzuki na jihar Arewa ta tsakiya a tsakanin shekarun 1973 zuwa 1975. Ya taba kasancewa mamba mai wakiltar mazabar arewa maso gabashin Zaria a Kaduna, ya kasance mai bayar da shawara ta musamman ga shugaban kasa Olusegun Obasanjo a kan abinci da tsaro a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003. Sai dai dan sa, Sadiq, an zabe sa ya wakilci mazabar Sabon Gari a majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam'iyyar PDP. Ya yi nasara a kan Garba Datti Muhammad na jam'iyyar APC wanda ke neman a zabe sa karo na hudu. Sadiq Abdullahi ya kasance daya daga cikin fasinjojin da 'yan ta'adda suka sace daga jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a wani hari da suka kai, ya yi kwanaki 69 a hannun su.


Bukar Abb-Ibrahim

Khadija Abba Ibrahim na wakiltar Damatura/Gujba/Gulani/Tarmuwa a majalisar jihar Yobe har karo biyu a shekarun 2007 zuwa 2015 kafin ta zama ministar kasashen waje ta cikin gida a tsakanin shekarun 2016 zuwa 2019. Ta dawo majalisar a karo na uku yanzu itace shugabar kwamitin majalisar a kan cigaban arewa maso gabas. An zabe ta a wani karon a karkashin jam'iyyar APC. Khadija ta auri Sanata Abba Bukar Ibrahim wanda shine gwamnan jihar Yobe a rusasshiyar jamhuriya ta uku a karkashin jam'iyyar SDP. Ya kara zama gwamna a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007. Abba Ibrahim ya koma majalisar dattijai a shekarar 2007 inda ya kasance a nan har zuwa shekarar 2019. A cikin shekarar 2017, ya taba fada a cikin majalisar dattijai, "Muna godiya matuka ga Allah da kuma 'yan Nijeriya. Bari in fadi wannan shugaban majalisar dattijai. Zan kasance a majalisar dattijai har sai lokacin da mutuwa ta raba mu. Kowa na cewa ni sanata ne na tsawon rayuwa ta, zan kasance a cikin majalisar dattijai na tsawon rayuwa..."


Blessing (David Mark)

Blessing Onuh na wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini ne a majalisar wakilai ta kasa daga jihar Benuwai. Mahaifinta shine shugaban majalisar dattijai, David Mark. Wani abu mai ban mamaki shine ta yi takara da yaron kawu ko gwaggon mahaifinta, Umahi Ahubi (tsohon kakakin majalisar wakilai ta jihar) domin samun tikitin jam'iyyar PDP a shekarar 2019 amma ba ta samu ba. Sai ta samu tikitin All Progressive Grant Alliance inda ta yi nasara a kan kawunta. Bayan ta rasa tikitin APGA ta koma APC, yanzu an sake zaben ta. Mahaifinta ya wakilce mazabar sanata ta kudancin jihar Benuwai daga shekarar 1999 zuwa 2019. A lokacin ya kasance shugaban majalisar dattijai na tsawon shekaru takwas (2007 to 2015). Ya kasance sanata da ya fi kowanne dadewa kawo yanzu. Shi Birgediya Janar ne mai ritaya kuma jigo a PDP, Mark ya kasance gwamnan soja a jihar Neja daga shekarar 1984 zuwa 1986 daga baya kuma ministan sadarwa a karkashin mulkin soja.


Beni (Solomon Lar) 

Beni, wadda lauya ce, ita ce babbar 'ya ga tsohon gwamnan jihar Filato, Solomon Lar. Yanzu an sake zaben ta domin wakiltar mazabar Langtan ta kudu da Arewa ta kasa karo na biyar. A zaben da ya gabata ta yi nasara a kan tsohon ministan wasanni na jam'iyyar SDP, Solomon Dalung. An zabe ta domin ta kasance a majalisar wakilai a shekarar 2007 kuma ta zamo shugabar kwamitin harkokin mata ta majalisar. A shekarar 2011 an sake zaben ta inda ta kasance shugabar kwamitin majalisar a kan hakkin bil-adama. A shekarar 2015 lokacin da ta ke mulki karo na uku, ta kasance shugabar kwamitin majalisar a kan kimiyya da fasaha, ta na kuma ruke da wannan matsayi har yanzun nan da ake da majalisa ta 9.

Moshood (Oba Akialo na Legas)

Moshood, wanda da ne ga Oba na Legas, Rilwan Akialo, an zabe shi domin ya wakilci mazabar kasa ta Lagos Island a majalisar wakilai ta kasa. Majalisar ta 10 za ta kasance mulkinsa karo na biyu kenan. Dan sarkin na Legas, wanda mamba ne a jam'iyyar APC, a yanzu haka shine mataimakin shugaban kwamitin majalisar a kan cigaban arewa maso gabas. 

Akeem (Alaafin Adeyemi) 

Daya daga cikin 'ya 'yan marigayi Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, an zabi Akeem a karo na uku kenan a majalisar wakilai. Yana wakiltar mazabar kasa Ajibio/Atiba/Oyo-East/Oyo-West a majalisar wakilai tun shekarar 2015. Wani abu da ya faru kuma shine a shekarar 2015, Akeem wanda ya ke a jam'iyyar APC sai kuma ya yi takara da wani da na Alaafin din, Bayo, wanda shi kuma ya ke a jam'iyyar PDP. 

Joshua (Jerry Gana)

Joshua da ne ga Farfesa Jerry Gana, tsohon ministan sadarwa a Nijeriya kuma sakataren jam'iyyar PDP lokacin kafuwar ta. Joshua ya yi nasara a zabe domin wakiltar mazabar Lavun/Mokwa/Edati daga jihar Neja a majalisar kasa. 


Babajimi (TOS Benson)

Mai wakiltar mazabar kasa ta Ikorodu a majalisar wakilai, Babajimi Benson ya fito ne daga babban iyali na 'yan siyasa. Babajimi na da alaka da Theophilus Owolabi Shobowale Benson, wanda aka fi sani da TOS Benson, shi babban lauya ne a Nijeriya, wanda ya ruke babbar sarauta ta Oba na Legas, ministan labaru, watsa labaru da al'adu, daga cikin matsayinsa kenan a jamhuriya ta farko.

Regina (George Akume)

Regina itace matar tsohon gwamnan jihar Benuwe kuma ministan ayyuka na musamman da alakar tsakanin gwamnati wato George Akume. An zabe ta domin wakiltar mazabar kasa ta Tarka/Gboko a majalisar wakilai, ta yi nasara ne a karkashin jam'iyyar APC. 

Erhriatake (James Ibori)

Erhriatake Ibori Sue-nu ta yi nasara a zaben mazabar kasa ta Ethiope da ke jihar Delta a karkashin jam'iyyar PDP. Ita 'ya ce ga tsohon gwamnan jihar Delta kuma ubangida ga jam'iyyar PDP a jihar, James Ibori.


Olumide (Olusegun Osobo)

Da ne ga tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osobo, an zabe shi a matsayin mai wakiltar mazabar Arewacin Abeokuta/Odeda/Obafemi-Owode da ke jihar Ogun a majalisar kasa ta 10 a karkashin jam'iyyar APC wadda mahaifinsa babba ne a cikin ta.


Ayodeji (Adebayo Alao-Akala) 

Olamiju Alao-Akala, da ga tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Alao-Akala, ya yi nasara a zaben mazabar Ogbomoso-North/Ogbomoso-South/Orire ta kasa domin wakiltar mazabar a majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam'iyyar APC.

No comments

Powered by Blogger.