Header Ads

Shugaba Buhari ya kara karfin dangantaka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran


Shugaba Buhari tare da Mataimakin shugaban kasar Iran

Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa mataimakin shugaban jamhuriyar Musulunci ta  Iran cewa Nijeriya a shirye ta ke wajen kara karfin dangantaka da ke tsakanin ta da Iran.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne yayin wata tattaunanwa a tsakaninsa da mataimakin shugaban kasar Iran, Mohsen Mansouri, ta waya, gabanin taron Majalisar Dinkin Duniya a Doha, babban birnin kasar Qatar. 

Buhari ya kara da cewa, "Na tattauna da mutanen Iran na lokaci mai tsawon kuma na san yadda suke musamman lokacin da na yi ministan man fatur.

"Saboda haka ina maraba da kara karfafa dangantaka a tsakanin kasashenmu domin kuwa muna da wuraren da muka hadu sosai, musamman a bangaren makamashi."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi maganar zaben da aka kammala a cikin kwanakin baya da bakon nasa, inda ya bayyana cewa sabon shugaban kasa zai karba mulki a cikin kasa da watanni uku, kuma yana fata alakar da ya kulla mai karfi a tsakanin kasashen biyu za ta cigaba da wanzuwa har a cikin gwamnatin da ke tafe. 

A nasa bangaren, mataimakin shugaban kasar ta Iran ya bayyana cewa ya yi matukar farin cikin haduwa da shugaban kasar Nijeriya, inda ya ce in an yi la'akari da cewa kasashen suna da yawan albarkatu na yawan jama'a da kuma albarkatun kasa, yana da kyau kasashen su hada hannu domin yin aiki tare musamman a bangaren aikin gona. 

Sakamakon takunkumi da Iran ke fuskanta a yanzu, mataimakin shugaban kasar ta Iran, Mr. Mansouri ya bayyana cewa a matsayinsu na shugabanni a yankunansu, yana da kyau yin aiki tare ya zamanto abinda ake dabbakawa a ko'ina domin gudun kadaici a duniya, inda ya bayyana cewa abinda ya kamata a yi shine a samar da wata hukuma wadda za ta kasance babba.

No comments

Powered by Blogger.