Header Ads

Satar mai: Kwamitin bincike ya bayar da rahotonsa

Wasu mutane na kwasar man da ke zubowa daga wani bututu

Kwamitin musamman kan binciken satar mai da rasa man da ake yi ya bayar da rahotonsa ga mai bayar da shawara a sha'anin tsaro na musamman, Babagana Monguno.

Shugaban sashen sadarwa na ofishin mai bayar da shawara a bangaren tsaro na musamman, Zakari Usman, ne ya bayyana haka a cikin wani jawabi da ya gabatar a ranar Talata, inda ya ce an bayar da rahoton a ranar Litinin. 

A yayin da ya ke mika rahoton, shugaban kwamitin, Mejo Janar Barry Ndiomu mai ritaya, ya bayyana cewa sun yi aiki tare da masu ruwa da tsaki na ciki da wajen masana'antar mai da iskar gas.

Mista Ndiomu ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki a bangaren gwamnatocin jihohi da ma'aikatu, jami'an tsaro, jami'an kula da dokoki, kamfanonin mai na cikin gida da na kasashen waje, masarautun gargajiya, al'ummun da ke dauke da man, matatun mai da sauransu duk an yi aiki tare da su.

Ya bayyana cewa kwamitin ya karba tare da yin duba ga rahotanni da rubuce-rubucen lokaci-zuwa-lokaci a kan satar mai da rasa mai da ake yi a lokuta da dama.

Kamar yadda ya bayyana, kwamitin ya gano matakai daban-daban na satar danyen mai duk da kokarin da sojoji da sauran jami'an tsaro ke yi domin kawo karshen satar man.

"Kwamitin ya gano cewa rasa man fetur da ake yi yana faruwa ne daga rashin samar da man da kyau, tace shi ba bisa ka'ida ba, sacewa daga kan rijiyoyin mai da kuma karkatar da shi daga bututun mai.

"Kwamitin har wa yau ya danganta rasa man da ake yi da rashin kyakkyawan ma'auni daga masana'anta da kuma tsaro wanda ba a shirya shi da kyau ba.

"Rudani dangane da rawar da masu alhaki kan al'amarin za su taka an bayyana shi shima a matsayin wani abu da ya taimaka wajen kara wahala dangane da gane masu sace mai da kuma rasa shi." Kamar yadda ya bayyana.

Mista Ndiomu ya yi kira da a tabbatar da an zartar da shawarwarin da ke cikin rahoton, inda ya bayyana cewa in har an zartar da shawarwarin, to satar mai da rasa shi za a kawo karshensu.

Ya bayyana cewa zartar da abinda ke cikin rahoton nan take ba zai kawai taimaka wajen kara hauhawar yawan man fetur da Nijeriya ke fitarwa ba ne domin cimma adadin da kungiyar kasashe masu fitar da mai OPEC ta shardanta mata ba ne, a'a, zai ma jawo ra'ayin masu saka jari kuma ya yi aiki ga tattalin arzukin Nijeriya da tsaron ta.

A yayin da ya ke karbar rahoton, mai bayar da shawara a bangaren tsaron ya yi godiya ga kwamitin domin yin aikinsa a lokacin da aka dibar masa da kuma warware al'amurran da kyau wadanda suka shafi satar mai da rasa shi.

Monguno ya tabbatar da cewa gwamnati za ta karanci rahoton da kyau kuma ta ga yadda za a tabbatar da shi, musamman shawarwarin da aka bayar wadanda ke da gajeren zango. 

Mai bayar da shawarar a bangaren sha'anin tsaro dama a ranar 6 ga watan Disambar 2022 ya rantsar da kwamitin binciken inda aka mika masa bangarori da dama da ake so ya yi bincike a kan su da suka shafi satar danyen man fetur da rasa shi a kowanne mataki.

Kwamitin ana tsammanin zai yi binciken satar mai da rasa shi da ake yi ne kuma ya kawo shawarwari yadda gwamnati za ta iya zartar da shawarwarin domin gwamnati ta dauki matakin kawo karshen laifuffukan da ake aikatawa a wannan masana'anta a cikin karamin lokaci.

An dai ba kwamitin sati goma ne domin kammala wannan aiki wanda za a fara daga ranar da aka kaddamar da kwamitin.

No comments

Powered by Blogger.